Sokoto: FG ta yi kira ga cibiyoyi da su mika tallafi ga wadanda harin 'yan bindiga ya shafa
Ma'aikatar jin kai da walwalar 'yan kasa ta yi kira ga cibiyoyin da ke karkashinta da su aika kayan tallafi da rage radadi ga jama'ar da suka tsallake harin 'yan bindiga na jihar Sokoto.
Ministar ma'aikatar, Sadiya Umar Farouq, a wata takarda da ta fitar, ta umarci cibiyoyin da ke da alhakin raba kayan rage radadi da su gaggauta kai dauki ga gwamnatin jihar Sokoto.
Ta yi Alla-wadai da kisan 'yan Najeriya da 'yan bindigar ke yi a yankunan karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.
Yayin jajantawa gwamnatin jihar da jama'ar jihar, ta mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu sakamakon mummunan harin.
Ta ce abin firgici ne yadda 'yan bindigar ke addabar yankuna masu tsananin zaman lafiya tare da halaka mutanen da basu ji ba balle gani.
KU KARANTA KUMA: Rikicin jam'iyyar APC: Tsohon kakakin majalisa ya aika wa Buhari muhimmin sako
A wani labarin na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da samar da 'yan sandan sa kai wadanda za su dinga aiki a karkashin kulawar jami'an 'yan sandan Najeriya da ke jihar.
Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa, a wata takarda da mai bada shawara ta musamman ga Matawalle a kan yada labarai, Zailani Bappa ya fitar, ya ce sabuwar cibiyar tsaron za ta tattara 'yan sa kai daga kananan hukumomi 14 na fadin jihar.
Kamar yadda Bappa ya bayyana, za a horar da 'yan sa kan ne a hukumar 'yan sandan Najeriya.
"Za a zaba matasa 700 don wannan aikin, 50 daga kowacce cikin kananan hukumomi 14 na jihar.
"Wannan sabon tsarin ya banbanta da tsohon tsarin 'yan sa kai na wadanda ke ruda al'amuran tsaro a baya.
"Sabon tsarin zai kunshi 'yan sa kai wadanda za a tantance kuma a horar da su karkashin hukumar 'yan sandan Najeriya kuma za a basu kayan aiki don a gano su da wuri.
"Aikinsu shine taya 'yan sandan Najeriya aiki a yankunansu," takardar tayi bayani.
Bappa ya ce tuni aka fara shirin kuma za a rantsar da kashin farko na 'yan sa kan nan babu dadewa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng