Sarkin Musulmi ya fadawa Gwamnatin Tarayya ta ba dakarun sojoji kayan aiki

Sarkin Musulmi ya fadawa Gwamnatin Tarayya ta ba dakarun sojoji kayan aiki

- Sultan na Sokoto, Muhammad Abubakar ya yi magana game da lamarin rashin tsaro

- Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira da Gwamnati ta tanadi kayan yaki da tsageru

- Sa'ad ya ce Sojoji ba su da kayan aikin da za su shiga kowane lungu da kwazazzabo

Mai alfarma Sultan Muhammad Saad Abubakar ya ce dole gwamnatin tarayya ta samar da kayan aiki ga rundunar sojin Najeriya domin a samu nasarar ganin bayan miyagu a kasar.

Alhaji Muhammad Abubakar ya bukaci gwamnati ta samar da duk wasu isassun makamai da kayan yaki da ake bukata domin lallasa tsagerun da ke tada zaune tsaye a Najeriya.

Sarkin Musulmi ya yi wannan jawani ne a ranar Asabar, 30 ga watan Mayu, 2020. Muhammad Abubakar ya fitar da wannan jawabi ne bayan jin an hallaka mutane a jihar Sokoto.

Idan ba ku manta ba a ‘yan kwanakin bayan nan wasu miyagun ‘yan bindiga su ka shiga kauyukan Sokoto, inda su ka kashe Bayin Allah fiye da 70 ba tare da an cafke su ba.

KU KARANTA: Wasu Miyagun 'Yan bindiga sun sace wani hamshakin Attajiri a gidansa

Sultan ya yi kuka da wannan abu, ya na mai bayyana cewa halin tsaro a kasar ya jagwalgwale. Alhaji Abubakar ya ce rashin tsaron da ake fuskanta a kasar ya munana a yanzu.

Mai alfarmar ya ce a yanzu mutane su na rayuwa ne cikin dar-dar din yiwuwar a hallakasu, ko kuma a sacesu ayi garkuwa da su. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto dazu.

“Mutane ba za su iya komawa aikinsu kamar yadda su ka saba ba a Najeriya. Rashin tsaro ya kai yanayin da ka na gidanka, sai wani ya shigo ya daukeka, ya yi gaba.” Inji Sultan Sa'ad.

Babban nauyin da ya rataya a kan duk wani shugaba da ke mulki shi ne ya kare rayuka da kuma dukiyar al’ummarsa. Sarkin Musulmin ya ja-kunnen duk masu rike da madafan iko.

A cewarsa, jami’an tsaro su na bukatar isassun kudin aiki idan har ana da niyyar kawo zaman lafiya. Abubakar ya ce dakarun kasar ba su da kayan aikin da za su iya shiga ko ina.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng