Bakar Guguwa Ta Taso a Amurka an Barke da Ruwa yayin da Wuta Ta Dauke
- Guguwa dauje da ruwan sama mai karfi ta haddasa katsewar wutar lantarki ga gidaje da wuraren kasuwanci kusan miliyan daya a Amurka
- An kuma samu cikas a zirga-zirgar jiragen sama, inda aka jinkirta tashin sama da jirage 2,000 tare da soke wasu fiye da 400
- Guguwar ta kuma tilasta dage bikin faretin ranar godiya ta Thanksgiving da ake gudanarwa duk shekara a birnin New York
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Guguwa da ruwan sama mai karfi ta haddasa katsewar wutar lantarki ga gidaje da wuraren kasuwanci kusan miliyan 1 a Amurka, yayin da aka samu cikas a harkokin sufuri a lokacin bikin Thanksgiving na ranar Alhamis.
Sama da gidaje da wuraren kasuwanci 900,000 ne suka rasa wutar lantarki a yammacin ranar Alhamis, inda akasarin wadanda abin ya shafa suke jihohin gabar tekun gabashin kasar.

Source: Getty Images
An ayyana dokar ta baci a jihohi
Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa an ayyana dokar ta baci a jihar New Jersey da wasu sassan jihar New York sakamakon guguwar.
Hukumar Kula da Yanayi ta Amurka ta kuma fitar da gargadin iska mai karfi ga arewacin jihar Georgia, mafi yawan yankin Mid-Atlantic da kudancin New England.
A birnin New York, magajin gari Zohran Mamdani ya ce an ceto wasu mutane biyu daga motocinsu bayan ambaliyar ruwa ta mamaye wuraren da suke.
Mamdani ya gargadi jama'a da su guji yin tafiya idan yanayin bai ba da damar hakan ba, yana mai cewa babu inda mutum zai je da ya fi kare lafiyarsa muhimmanci.

Source: Getty Images
An samu cikas a jiragen sama
Guguwar ta kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen sama a fadin Amurka, inda bayanan kamfanin bibiyar jirage na FlightAware suka nuna cewa an jinkirta tashin sama da jirage 2,000 da ke tashi daga ko zuwa kasar.
BBC ta wallafa cewa hukumomi sun kuma soke sama da jirage 400 sakamakon mummunan yanayin.
A jihar Maryland, an bukaci kusan jama'a miliyan biyu da ke kananan hukumomin Montgomery da Prince George's da su rage amfani da ruwa saboda katsewar wutar lantarki da ruwan sama mai karfi ya haddasa.
A yankin Midwest, dusar kankara mai yawa ta sauka a ranar Alhamis, inda wasu wurare a jihar Missouri suka samu dusar kankara mai kaurin santimita 35.
Haka kuma, an samu gargadin yiwuwar guguwa mai karfi a wasu yankuna, ciki har da wata guguwar da ba kasafai ake gani ba a kudu maso gabashin birnin Seattle na jihar Washington.
Trump zai gana da El-Sayed
A wani labarin, kun ji cewa Donald Trump ya ce yana shirin ganawa da zababben sanatan Michigan, Abdul El-Sayed, domin tattauna shirin samar da kiwon lafiya ga kowa a Amurka.
El-Sayed ya nemi a sauya sunan shirin da ake kira “Medicare for All” zuwa “Trumpcare”, da nufin jawo hankalin Trump ya goyi bayan shirin.
Trump ya bayyana cewa El-Sayed mutum ne mai basira, yana mai cewa yana ganin akwai yiwuwar su cimma matsaya mai kyau kan batun.
Asali: Legit.ng

