Gwamnan Edo Ya Musanta Hannunsa a Harin da Aka Kai wa Magoya Bayan NDC
- Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya maida martani bayan an fara zarginsa da hannu a harin da aka kai wa magoya bayan NDC a Benin City
- Okpebholo ya bayyana cewa a tarihin siyasarsa bai taba amfani da yan daba domjn tsoratar da abokan hamayya ba
- Hakan dai na zuwa ne bayan waus maharan sun bude wa ayarin Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wuta bayan sun isa jihar Edo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya musanta zargin da ake yi na cewa yana da hannu a harin da aka kai wa magoya bayan jam’iyyar NDC a birnin Benin.
Okpebholo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani gangamin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Ehor, hedikwatar ƙaramar hukumar Uhunmwonde.

Source: Facebook
Hakan ya faru ne kwana guda bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kan magoya bayan NDC da suka taru a kan titin Airport Road domin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar, Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Kwankwaso.
Gwamnan Edo ya musanta hannu a harin
Gwamnan ya bayyana zarge-zargen da ake masa a matsayin ƙarya, yana mai jaddada cewa bai taɓa amfani da ’yan daba a lokacin yaƙin neman zaɓensa na baya ba.
“Jiya wasu mutane suna kuka saboda sun yi tunanin za su zo Edo su yi fice, amma da suka zo, sai suka tarar da mutane uku kacal a cikin zauren taro.
"Sai suka fara jifarmu da maganganu saboda suna son ɓata mana suna. Suka fara ambaton sunana, amma ni ba ni da lokacin kowa. Ƙarya suke yi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jin an ambaci sunansa a wani rahoton talabijin ya sa ya fahimci cewa zarge-zargen da ake yaɗawa a kansa ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu
Okpebholo ya tuna tarihin siyasarsa
Okpebholo ya kuma musanta amfani da ’yan daba a lokacin yaƙin neman zaɓensa, inda ya tuna da lokacin da ya tsaya takarar sanata da kuma gwamna.
“Lokacin da na tsaya takarar sanata, ban yi amfani da ’yan daba ba. Lokacin da na tsaya takarar gwamna ma, ban yi amfani da ’yan daba ba,” in ji shi.

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa shugaban NDC na cikin waɗanda aka taɓa dangantawa da kisan ɗan sandansa a baya, amma ya ce ya ƙaurace wa bin lamarin domin kada a zarge shi da amfani da siyasa wajen gallaza wa wasu.
“Shugaban NDC yana cikin waɗanda aka nuna da hannu a wancan lokacin. Idan na fara ɗaukar mataki yanzu, za su ce ina gallaza musu ne saboda siyasa," in ji shi.
An kai wa mambobin NDC hari
Kun ji cewa an shiga yanayin tashin hankali a Benin City, jihar Edo, bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar NDC.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin maharan sun farmaki mambobin NDC da suka taru a kan titin filin jirgin sama domin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso .
Asali: Legit.ng
