Kaddamar da sabon atisaye: Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a Sokoto tare da lalata sansaninsu

Kaddamar da sabon atisaye: Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a Sokoto tare da lalata sansaninsu

Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta sanar da cewa ta kashe dumbin 'yan bindiga tare da lalata sansaninsu a wani sabon hari da ta kaddamar daga sararin samaniya a kan 'yan bindiga a jihar Sokoto.

Darektan hulda da jama'a na rundunar NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Daramola ya ce babban hafsan rundunar sojojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya sanar da cewa an kai hari sansanin 'yan bindigar ne ranar Litinin a karkashin atisayen HADARIN DAJI.

A cewar Abubakar, kaddamar da babban atisayen 'ACCORD' na daga cikin kokarin rundunar soji na kawo karshen ta'addancin 'yan bindiga, barayin shanu, ma su garkuwa da mutane da sauran batagari da ba sa son zaman lafiya.

Bayan ya nuna jin dadinsa da kai sabon harin, Abubakar ya ce manufar atisayen shine yi wa 'yan bindiga ruwan wuta har sai sun fito daga maboyarsu da ke dajin Kagara a jihar Sokoto.

Ya bayyana cewa dakarun NAF su na aiki bisa hadin gwuiwa tare da takwarorinsu na kasa domin tabbatar da cewa babu wasu 'yan bindiga da su ka tsira bayan an yi kuguden wuta a sansaninsu daga sararin samaniya.

A cewar Abubakar, saboda dajin Kagara ya ratsa har cikin kasar Nijar, rundunar sojin Najeriya ta na aiki tare da dakarun kasar domin tabbatar da cewa 'yan bindigar ba su sulale ta iyakar Najeriya da Nijar ba.

Babban hafsan ya ce an tura dumbin dakarun NAF zuwa Sokoto ne domin kara karfin yaki da 'yan ta'adda da rundunar soji ke yi a jihar da kewaye.

Kaddamar da sabon atisaye: Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a Sokoto tare da lalata sansaninsu
Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a Sokoto
Asali: Twitter

A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa ta kashe dumbin mayakan kungiyar Boko Haram.

A kashe mayakan ne yayin wani luguden wuta da jiragen yaki na rundunar NAF suka yi a sansanin mayakan da ke Parisu da Bula Bello a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

DUBA WANNAN: Katsina: 'Yan bindiga sun kai hari a daidai lokacin da Buratai ke kaddamar da sabon atisaye

Manjo Janar John Enenche, shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar da safiyar ranar Litinin.

A cewar Janar Enenche, rundunar soji ta kai harin ne; "ranar 3 ga watan Yuli a cigaba da atisayen rundunar soji na karasa murkushe mayakan kungiyar Boko Haram bayan samun bayanan sirri a kan wasu sansani da mayakan ke buya.

"Rundunar soji ta aika jiragenta na yaki bayan tabbatar da cewa mayakan suna buya a sansani. Jiragen sun yi luguden wuta, sun saki bamabamai da makamai ma su linzami a sansanin.

"Dumbin mayakan kungiyar sun mutu, sannan an lalata sansaninsu yayin ruwan wutar da jiragen suka yi," a cewar wani bangare na jawabin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel