Zamfara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan bindiga, sun saki bam a kogon Hassan Tagwaye a dajin Damborou

Zamfara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan bindiga, sun saki bam a kogon Hassan Tagwaye a dajin Damborou

Dakarun rundunar sojin sama a karkashin atisayen HADARIN DAJI sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi da 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma, musamman a jihohin Katsina, Sokoto, da Zamfara.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun, manjo janar John Enenche, rundunar soji ta sanar da cewa ta lalata sansani biyu na 'yan bindiga da wani kogo da mambobin kungiyar 'yan bindiga a karkashin jagorancin Hassan Tagwaye ke buya a dajin Doumborou da ke jihar Zamfara.

A cewar sanarwar, rundunar soji ta ce ta kashe manyan kwamandoji da mambobin kungiyar 'yan bindiga ta hanyar yi musu luguden wuta a sansaninsu a ranar 23 ga watan Yuni, 2020.

Rundunar soji ta ce ta kai harin ne bayan samun sahihan shaidun gani da ido daga na'urar leken asiri (ISR) wacce ta leko sansani da wuraren boye makaman 'yan bindiga da kuma kogon da suke buya domin fakewa idan an kawo musu hari.

Zamfara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan bindiga, sun saki bam a kogon Hassan Tagwaye a dajin Damborou
Zamfara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan bindiga, sun saki bam a kogon Hassan Tagwaye a dajin Damborou
Asali: Twitter

Bayan tabbatar da shaidun ne sai rundunar soji ta aika da jirgin yaki mai karfin aman wuta zuwa dajin domin kaddamar da hari a kan 'yan bindigar da sansaninsu da sauran wuraren buyansu da boye makamai.

DUBA WANNAN: Abun tausayi: Bidiyon masu kukan mutuwar tsohon gwamna Ajimobi a gidansa na Ibadan

A cewar Enenche, binciken rundunar soji ya tabbatar da cewa an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Hassan Tagwaye tare da dan uwansa Hussain Tagwaye yayin harin.

Kazalika, an kashe wasu 'yan bindigar da dama tare da raunata wasu da ake zargin sun tsere duk da sun samu raunuka.

Rundunar soji ta bukaci mazauna yankin su saka ido domin kai rahoton duk wani mutum da aka gani da sabon rauni mai cike da alamomin tambaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng