Ta'addanci a arewa: 'Ba zamu bari haka ta cigaba da faruwa ba' - Rundunar soji ta fusata
Rundunar sojojin Najeriya ta ce zata bi diddigin mayakan kungiyar Boko Haram/ISWAP da 'yan bindigar Katsina da Sokoto duk inda suke tare da hallakasu.
A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta, rundunar soji ta ce ranta ya baci da harin da 'yan Boko Haram/ISWAP suka kai tare da kashe mata da kananan yara a kauyen Faduma Koloram da ke yankin karamar hukumar Gubio a jihar Borno.
"Tuni an tura rundunoni zuwa yankin domin kashe wadanda suka kai harin ko kuma a kamasu. Mun aika sakon gaggawa zuwa ga kwamandan rundunar atisayen Ofireshon Lafiya Dole a kan a tsaurara matakan tsaro a yankin domin kare rayukan jama'a.
"Kazalika, rundunar soji tana sane da al'amuran 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma, musamman a jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara.
"Mun fuskanci cewa wasu daga cikin 'yan bindigar da aka fatattaka daga Katsina sun yi kaura zuwa makwabtan jihohi tare da kai hari a kan fararen hula.
"Mu na mika sakon jaje da ta'aziyya ga jama'ar Najeriya, musamman na jihohin Borno, Katsina, Sokoto da Zamfara.
"Mu na masu baku tabbacin cewa ba zamu bari ba, sai mun kawar da dukkan 'yan ta'adda masu cutar da jama'a," a cewar jawabin; mai dauke da sa hannun kanal Sagir Musa, mukaddashin kakakin rundunar soji.
DUBA WANNAN: Dabiu'u 10 na yau da kullum da ke sukurkuta kwakwalwa
Rundunar soji ta ce zata hada kai da rundunar sojojin sama da sauran hukumomin tsaro a jihohin da ke fama da matsalolin domin a tabbatar da dawowar zamana lafiya, kamar yadda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni.
Kazalika, rundunar sojin ta bayar da tabbacin cewa ba zata bar irin wannan aikin ta'addanci ya cigaba da faruwaba ba tare da ta nuna fushinta a kan 'yan ta'adda ba, a ko ina suke a fadin Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng