Matakin da Majalisa ke Shirin Dauka domin Takawa Yan Sandan Jihohi Birki
- Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce Majalisar Tarayya na shirin kawo sabuwar doka
- Bamidele ya ce sabuwar dokar za ta samar da ka'idojin da za su hana gwamnonin jihohi amfani da 'yan sandan jihohi wajen muzgunawa abokan hamayya
- Sanatan ya ce dokar za ta fayyace iyakokin ikon 'yan sandan tarayya da na jihohi, tare da bayyana yadda za a gudanar da ayyukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana shirin majalisar na kawo sabuwar doka kan yan sandan jihohi.
Bamidele ya bayyana cewa Majalisar Tarayya na aiki tare da bangaren zartarwa wajen samar da wata sabuwar doka domin hana amfani da 'yan sandan jihohi ta hanyar da ba ta dace ba.

Source: Facebook
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai na majalisar kan fargabar cin zarafi a jihohi, cewar TheCable.
Ana fargaba kan yan sanda jihohi
Ana fargabar gwamnonin jihohi za su iya amfani da rundunonin 'yan sandan jihohinsu wajen tsoratar da abokan hamayyarsu na siyasa.
Sanatan ya ce dokar da ake shiryawa za ta samar da tsare-tsare da ka'idojin gudanar da ayyukan 'yan sandan jihohi, ba tare da la'akari da jam'iyyar siyasar da ke mulki ko mutumin da ke jagorantar jihar ba.
Ya bayyana cewa jam'iyyar da ke kan mulki a yau za ta iya komawa jam'iyyar adawa nan gaba, haka kuma jam'iyyar adawa za ta iya samun damar mulki a wani lokaci.
A cewarsa, saboda haka akwai bukatar samar da dokoki masu inganci da za su ci gaba da aiki ba tare da la'akari da sauyin jam'iyya ko shugabancin siyasa ba.

Source: Facebook
Majalisa ta na tattaunawa kan matsalar
Bamidele ya amince cewa har yanzu akwai fargabar yiwuwar amfani da 'yan sandan jihohi ba bisa ka'ida ba, duk da amincewa da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ya shafi kafa rundunonin 'yan sandan jihohi.
Ya ce Majalisar Tarayya na tattaunawa da bangaren zartarwa kan wani sabon kudirin doka da aka tsara tare da shigar da masu ruwa da tsaki domin fayyace yadda rundunonin za su gudanar da ayyukansu.
Sanatan ya bayyana cewa dokar za ta fayyace nauyin da ke rataye a wuyan hukumar kula da aikin 'yan sanda, da kuma yadda rundunonin 'yan sandan tarayya da na jihohi za su yi aiki tare.
Ya kuma ce za a fayyace iyakokin ikon kowace runduna, domin kauce wa rikice-rikice kan wanda ke da hurumin daukar mataki a wani yanayi, cewar Vanguard.
Bamidele ya gabatar da wasu tambayoyi kan yadda tsarin zai kasance, ciki har da ko kowace jiha za ta samu hukumar kula da aikin 'yan sanda ta kanta, da kuma wanda zai jagoranci irin wannan hukuma.
Gwamnati ta ware N140bn ga yan sanda
An ji cewa Majalisar NEC ta amince da ƙarin Naira biliyan 130 domin gyara da inganta cibiyoyin horas da jami’an ’yan sanda a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan
Tinubu Ya Tuna da Iyalan Sojojin da Suka Mutu a Hatsarin Jirgi, Ya ba Su Abin Duniya
Sabon tallafin ya kai kuɗin shirin zuwa Naira biliyan 230, yayin da gwamnati ke shirin ɗaukar sababbin jami’an ’yan sanda 50,000.
Majalisar ta kuma amince da ayyukan raya ƙasa biyu da Bankin Duniya zai tallafa wa da dala biliyan 850 domin inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Asali: Legit.ng

