Harin 'yan bindiga: Mutane fiye da 5000 a ƙauyuka 8 sun tsere a Sakkwato

Harin 'yan bindiga: Mutane fiye da 5000 a ƙauyuka 8 sun tsere a Sakkwato

Sakamakon hare-haren 'yan bindiga da ya tsananta a wasu kauyuka na karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato, mutane fiye da dubu 5 sun ranta na kare domin neman mafaka.

Dubunnan mutane a wasu kauyuka takwas na karamar hukumar, sun tsere daga muhallansu a yayin da 'yan daban daji ke daukan fansa kan matsin lambar kakkabe su da dakarun soji ke yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a baya bayan nan rundunar sojin sama ta yi amfani da jirage wajen yin ruwan wuta a kan sansanan 'yan daban Daji a Dajin Kagara daura da kananan hukukomin Isa da Sabon Birni.

Rahotanni sun bayyana cewa, da dama daga cikin 'yan daban dajin sun tsere kauyuka na kusa sakamakon hare-haren dakarun sojin, inda suka sake yin kungiya tare da kai hari wasu kauyukan.

Shugabannin tsaro na Najeriya
Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Shugabannin tsaro na Najeriya Hakkin mallakar hoto; Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

An ruwaito cewa, baya ga balle shaguna da diban dukiya, masu ta'adar sun kuma kashe mutane 6 tare da yin awon gaba da daruruwan dabbobi a kauyukan da suka kai hare-haren.

Masu bayar da shaida ga manema labarai sun zayyano al'ummomin da abin ya shafa wanda sun hadar da Bafarawa, Arune, Suruddudu, Sabon Garin Lugu, Tsillawa, Gwalama da Dan Adama, wanda duk suke karkashin karamar hukumar Isa.

Wani mutumi daga daya daga cikin ƙauyukan da ya bukaci a sakaya sunansa,ya ce an kashe mutane biyu a ƙauyukan Tsillawa da Suruddudu da uku a ƙauyen Gebe.

KARANTA KUMA: Zaben Gwamnan Ondo: APC ta tantance Akeredolu da manema takara biyar

Ya kara da cewa, a yanzu haka an bar ƙauyukan fayau bayan da kimanin mutane dubu biyar suka tsere zuwa garin Isa ko Shinkafi na jihar Zamfara, yayin da wasu suka fake a gidajen 'yan uwansu a wasu wuraren daban.

A bangare guda kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, rundunar 'yan sanda sun kama wani Francis Diamond da ake yi wa lakabi da Iron Man, shugaban wata mugunyar kungiyar asiri ta Aiye a jihar Legas.

An kama Diamond ne bayan wasu hare hare da kisar kai da fashi da makami da aka yi a unguwanin Ajah da Epe a jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Legas ta danganta laifukan da aka aikata da kungiyar asirin ta wanda ake zargin.

'Yan sandan sun kuma kama wasu mambobin kungiyar takwas a sassa daban na Ikorodu bayan shugaban kungiyar ya bayyana musu inda suke.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel