Jihohi masu talauci: Tambuwal ya yi watsi da rahoton NBS
- Gwamna Aminu Tambuwal, na jihar Sokoto, ya musanta rahoton hukumar kididdiga ta kasa na cewa jiharsa na daya daga cikin jihohin da suka fi kowanne talauci a Najeriya
- Kamar yadda NBS ta fitar da rahoton a watan Afirilun 2020, ta ce jihar Sokoto ce ta 9 a jerin jihohi 10 da talauci ya samu wurin zama a kasar
- Tambuwal ya ce gwamnatin jihar za ta bibiyi al'amuran NBS kuma ta ga yadda za ta bayyana wani rahoton
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya musanta rahoton hukumar kididdiga ta kasa na cewa jiharsa na daya daga cikin jihohin da suka fi kowanne talauci a kasar nan.
Tambuwal ya yi wannan maganar ne bayan rahoton da ya samu mai taken "Tsarin habbaka Sokoto: 2020-2025 a gidan gwamnatin jihar."
Kamar yadda NBS ta fitar da rahoton a watan Afirilun 2020, ta ce jihar Sokoto ce ta 9 a jerin jihohi 10 da talauci ya samu wurin zama a Najeriya daga yankin arewa. Sokoto, Taraba da Jigawa ne ke kan gaba.
"Ban so shiga wannan al'amarin na NBS ba amma ina kira gare su da su sake duba jihohi masu talauci sannan su yi bayanin yadda jihar Sokoto ta shiga ciki," gwamnan yace.
Ya kara da cewa: "Mun san cewa tabbas akwai nakasa ko kuma kuskure a wannan kididdigar.
"Idan ka duba irin shirye-shiryen mu a jihar Sokoto, na jama'a ne. Na tallafi ne ga masu talauci.
"Ko abinda muke yi ta hukumar Zakka da Waqfi kadai, na san babu jihar da ke yin kamarsa."
KU KARANTA KUMA: Babu mamaki wani na’u’in COVID-19 ya bulla a kasar nan - Masana
Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta bibiyi al'amuran NBS kuma ta ga yadda za ta bayyana wani rahoton, Sahara Reporters ta ruwaito.
"Za su fitar da wanda ke bayyana jihar Sokoto a cikin matalauta ko a'a.
"Mun aminta cewa mu ba masu talauci bane kuma hakan zai bayyana," gwamnan yace.
A gefe guda, mun ji cewa sakamakon annobar korona, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalharatu Bafarawa ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati a Najeriya da su sadaukar da wani kaso a albashinsu don bai wa gwamnatocin tarayya da na jiha damar tallafi ga 'yan Najeriya da basu aiki.
Tsohon gwamnan yayin magana a kan yadda annobar korona ta zama ruwan dare a duniya, ya ce ta tada hankulan jama'a a fadin duniya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng