Bayan Kayar da APC, Gwamnan Jihar Osun Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Karo na 2

Bayan Kayar da APC, Gwamnan Jihar Osun Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Karo na 2

  • Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya karbi rantsuwar kama aiki a wa’adinsa na biyu bayan lashe zaben 2026
  • Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa bikin rantsarwar a madadin Shugaba Tinubu
  • Adeleke ya bayyana manufofinsa na wa’adi na biyu, ciki har da bunƙasa lafiya, samar da wutar lantarki, gyaran hanyoyin ruwa da masana’antu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osogbo, jihar Osun – Ademola Adeleke ya karbi rantsuwar kama aiki a wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Osun, inda ya yi alƙawarin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar jihar.

An rantsar da Adeleke ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, 2026 a filin wasa na Osogbo City Stadium, tare da mataimakinsa, Prince Kola Adewusi.

Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke lokacin da yake rantsuwar kama aiki a Osogbo Hoto: Mathew Adeniji
Source: Facebook

Alƙalin alkalan jihar Osun, Mai shari’a Adepele Ojo, ce ta jagoranci rantsarwar, kamar yadda rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

An sako Peter Obi a gaba, ana so ya janyewa Tinubu takarar 202

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa wajen bikin a madadin Shugaba Bola Tinubu.

Gwamna Adeleke ya fadi shirin gwamnatinsa

A jawabin da ya gabatar bayan rantsuwar kama aiki, Adeleke ya bayyana sake zaɓensa a matsayin “nasarar muradin al’umma” da kuma abin koyi a ƙasa wajen jajircewa kan dimokuraɗiyya.

Ya bayyana cikakken shirin gwamnatinsa na wa’adi na biyu, wanda ya mayar da hankali kan jin daɗin jama’a, faɗaɗa ababen more rayuwa, bunƙasa masana’antu, sauya fasalin noma, tattalin arzikin zamani, yawon buɗe ido da ci gaban matasa da mata.

Gwamnan ya yi alƙawarin sauya tattalin arzikin jihar Osun daga wanda ya dogara da ayyukan ma’aikatan gwamnati zuwa cibiyar masana’antu.

Tinubu ya sa baki kan kudin Osun

Adeleke ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya sa baki a rikicin da ya shafi rabon kuɗaɗen ƙananan hukumomi, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa za a warware matsalar baki ɗaya cikin mako guda mai zuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta tabbatar da kashe mutum kusan 100 a jihar

Ya ce gwamnatinsa ta riga ta gyara tare da samar da kayan aiki a cibiyoyin kula da lafiya matakin farko (PHCs) guda 232 cikin 332, inda aka sanya musu na’urorin samar da hasken rana da wutar lantarki a wa’adinsa na farko.

Sai dai ya ce rike kuɗaɗen ƙananan hukumomi ya kawo tsaiko ga kammala aikin a sauran cibiyoyin.

Adeleke ya tabbatar da cewa:

“Da zarar an warware wannan matsala, gwamnatina za ta tabbatar da gyara sauran cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 102.”

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ci gaba da biyan albashin malaman makarantun firamare, ma’aikatan lafiya matakin farko da yan fansho daga ƙananan hukumomi a cikin shekaru biyu da suka gabata, duk da ƙalubalen kuɗaɗe.

Gwamnan ya kuma yi alƙawarin inganta manyan asibitocin gwamnati, ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya da kuma faɗaɗa samar da magunguna a faɗin jihar.

Adeleke ya kulla yarjejeniya da APC?

Kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke ya musanta cewa ya yi yarjejeniya da APC kan rabon kujerun majalisa da shugabancin ƙananan hukumomi a Osun.

Ya jaddada cewa fahimtar siyasar da ke tsakaninsa da fadar shugaban ƙasa ba ta ƙunshi wata yarjejeniya ta raba muƙaman zaɓe da APC a Jihar Osun ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262