FIAP da FactCheckAfrica Sun Yi Taro domin Yakar Barazanar Labaran Karya a Afrika

FIAP da FactCheckAfrica Sun Yi Taro domin Yakar Barazanar Labaran Karya a Afrika

  • Fundación para la Internacionalización de las Administraciones Públicas (FIAP) ta hada taro domin a ga bayan labaran karya
  • FIAP ta yi wannan ne da hadin-kan FactCheckAfrica a karkashin wata gudunmuwa da kungiyar EU ta ke ba kasashen ECOWAS
  • Wannan yana cikin yunkurin da ake yi da taimakon kasashen Turai na tabbatar da an yi zabuka lafiya a Najeriya da makwabtanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Fundación para la Internacionalización de las Administraciones Públicas (FIAP) da FactCheckAfrica sun shirya taro na kasa da kasa.

An yi wannan zama ne da ‘yan jaridu, masu bankado labaran karya, kungiyoyi masu zaben kansu, masana fasahar zamani da matasa daga kasashe.

FactCheck Africa
Taron kasa da kasa da FIAP da FactCheckAfrica suka shirya a Abuja Hoto: FactCheck Africa
Source: Facebook

Taro domin yakar yaduwar labaran bogi a Afrika

FactCheckAfrica ta ce makasudin taron shi ne ganin yadda masu ruwa da tsaki daga Najeriya, Gambia da Jamhuriyyar Benin za su yaki labaran bogi.

Cibiyar tana daukar kirkirarrun labarai da na karya a matsayin barazana ga sha’anin zabe musamman da ake jiran zabuka a Gambiya da Najeriya.

An yi taron ne a ranakun 24 da 25 ga watan Nuwamban 2026 a otel din Lake Greenfield Hotel, Kado, Abuja.

Zaman da aka shirya a dalilin gudumuwar EU ga shirin ECOWAS ya ba masu ruwa da tsaki damar duba yadda za a yi maganin labaran karya a kasashen.

Cibiyar FIAP ta hada-kai da FactCheckAfrica a Najeriya, Banouto a Jamhuriyyar Benin da Gambia Participate a kasar Gambiya wajen cin ma burinsu.

Shugaban hukumar zabe ya halarci taron

Cikin wadanda suka halarci taron har da Sakataren yada labarai na shugaban INEC, Mr Dayo Oketola wanda shi ya wakilci Joash Ojo Amupitan.

Farfesa Joash Amupitan ya yi bayanin kokarin hukumar INEC wajen ganin an yi maganin yada labarai marasa inganci yayin da ake shirin zabe.

Ya ba da misalin yadda aka rika yada labaran karya yayin da shugaban INEC ya ziyarci Chatham House.

Shugaban FactCheckAfrica, Abideen Olasupo, ya koka game da yadda ake amfani da sauran harsunan gida wajen yada labaran karya a nahiyar.

Saboda haka ne Abideen Olasupo ya ce cibiyarsa ta ke kokari domin tabbatar da cewa jama’a suna samun labarai na gaskiya dangane da harkar zabe.

Kasashen Turai suna goyon bayan yunkurin

Jakadu da wakilan kungiyar Turai da kasashen Sifen, Denmark da Jamus sun yi magana da murya daya a yunkurin magance yada labarai marasa tushe.

Massimo De Luca wanda shi ne shugaban tawagar EU da ECOWAS a Najeriya ya ce nauyin ganin bayan wannan matsala yana kan ‘yan jarida da gwamnati.

Shi ma Jakadan Sifen, Mr Félix Costales ya yi wannan kira amma yake cewa dole a yi hattara ka da a toshe wa jama’a hakkinsu a kokarin yakar matsalar.

Ganin yadda aka tara matasa daga kasashen Afrika ta yamma ya burge babbar jami’ar jakadancin kasar Denmark a Najeriya, Mrs Julie Rosenkilde Hannibal.

Rosenkilde Hannibal ta ce Denmark za ta cigaba da goyon bayan shirin EPSG domin matasan su fito da dabarun da za su yi aiki a kasashen yammacin Afrikan.

Wajen taron aka kaddamar da shafin Elect Peace (electpeace.org) da cibiyar Dataphyte Foundation ta kirkira domin hada kan kungiyoyi masu zaman kansu.

Kafin a gama zaman kwanaki biyun, an saurari jawabi kuma an yi tattauna dabam-dabam saboda ganin yadda za a bullo wa lamarin da aka sa a gaba.

Karin bayani game da taron kamar yadda cibiyar FactCheck Afrika ta wallafa a Facebook.

An yi baja-kolin fasaha a taron Fact Check Africa

Labari ya zo cewa gidauniyar FIAP da kungiyar FactCheckAfrica sun shirya wani taron kwanaki biyu a Abuja don yaki da labaran karya gabanin zaben 2027.

Matasa daga jihohi kamar Legas, Kano, da Enugu sun baje kolin dabaru irin su zane, bidiyoyi, wakoki, da shafukan yanar gizo masu fallasa labaran bogi.

A wajen taron da ya samu halartar wakilan kungiyoyin EU da ECOWAS, FactCheckAfrica ta kaddamar da ka’idoji 10 na amfani da kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng