Hotuna: Shugaban sojin saman Najeriya ya kai ziyara Sokoto
- Babban hafsan rundunar sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya ziyarci jihar Sokoto
- Ya kai ziyarar ne don ganin yadda al'amuran tsaro ke faruwa tare da duba bukatar kirkiro wasu sabbin tsarikan da za a halaka 'yan bindiga tare da murkushe al'amuransu a jihar
- Shugaban sojin ya kuma ba Sultan na Sokoto da Gwamna Tambuwal tabbacin daukar tsatsauran mataki kan miyagu a jihar
Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya kai ziyara jihar Sokoto.
Ya ziyarci jihar ne don ganin yadda al'amuran tsaro ke faruwa tare da duba bukatar kirkiro wasu sabbin tsarikan da za a halaka 'yan bindiga tare da murkushe al'amuransu a jihar Sokoto.
Kamar yadda rundunar sojin saman ta wallafa a shafinta na twitter, Shugaban hafsan sojin saman ya ba sarkin Musulmi, Sultan Abubakar da Gwamna Aminu Tambuwal tabbacin daukar tsatsauran mataki a kan yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.
Ta ce: “Shugaban rundunar sojin saman Najeriya ya kai ziyarar ganin yadda al'amuran tsaro ke faruwa a jihar Sokoto, ya ba Sultan Abubakar, Gwamna Tambuwal tabbacin daukar mummunan mataki a kan yan bindiga da sauran masu aikata miyagun ayyuka.”
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Oshiomhole ya bayyana irin zaben fidda gwanin da za a yi a Edo
A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa ma'aikatar jin kai da walwalar 'yan kasa ta yi kira ga cibiyoyin da ke karkashinta da su aika kayan tallafi da rage radadi ga jama'ar da suka tsallake harin 'yan bindiga na jihar Sokoto.
Ministar ma'aikatar, Sadiya Umar Farouq, a wata takarda da ta fitar, ta umarci cibiyoyin da ke da alhakin raba kayan rage radadi da su gaggauta kai dauki ga gwamnatin jihar Sokoto.
Ta yi Alla-wadai da kisan 'yan Najeriya da 'yan bindigar ke yi a yankunan karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.
Yayin jajantawa gwamnatin jihar da jama'ar jihar, ta mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu sakamakon mummunan harin.
Ta ce abin firgici ne yadda 'yan bindigar ke addabar yankuna masu tsananin zaman lafiya tare da halaka mutanen da basu ji ba balle gani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng