Girma Ya Kwaɓe: An Tura Tsohon Gwamna Gidan Yari kan Hallaka Budurwarsa

Girma Ya Kwaɓe: An Tura Tsohon Gwamna Gidan Yari kan Hallaka Budurwarsa

  • Tsohon gwamnan jihar Migori a Kenya, Zacharia Okoth Obado, ya shiga gidan yari na tsawon shekaru 25 bisa samunsa da hannu a kisan kai
  • An yanke wa Obado hukuncin ne tare da wasu tsofaffin hadimansa biyu, Michael Oyamo da Caspal Ojwang' Obiero, bisa tuhume-juhume
  • Kotun ta tabbatar da cewa Obado ne ya samar da dalilin aikata kisan tare da kudaden gudanar da shi, yayin da hadimansa suka taimake shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Nairobi, Kenya - Wata babbar kotu a Kenya ta yanke wa tsohon gwamnan Migori, Zacharia Okoth Obado, hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari.

Ana zargin dan siyasar ne da hannu a kisan wata dalibar jami'a mai juna biyu da aka yi a shekarar 2018.

An tura tsohon gwamna zuwa gidan yari
Tsohon gwamna a Kenya, Zacharia Okoth Obado da aka daure a gidan yari. Hoto.
Source: Facebook

Binciken da BBC ta yi ya nuna cewa Obado da marigayiyar suna da alakar soyayya, wadda ta kai ga samun cikin watanni bakwai. Rahoton ya ce tsohon gwamnan bai ji dadin cikin ba.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma'a, tare da hukunta wasu tsoffin hadimansa biyu, wadanda aka samu da hannu wajen shirya kisan Sharon Belyne Otieno mai shekaru 26.

Kotun ta yanke wa tsohon mai taimaka wa Obado, Michael Oyamo, hukuncin daurin shekaru 25, yayin da tsohon magatakardan karamar hukumar, Caspal Ojwang' Obiero, zai shafe shekaru 18 a gidan yari.

Alkalin kotun, Cecilia Githua, ta bayyana cewa Obado ne ya samar da dalilin kisan tare da kudaden gudanar da shi, yayin da Oyamo ya tsara yadda za a aiwatar da shirin.

Haka kuma, kotun ta ce Obiero ya bayar da gudunmawa wajen samar da kayayyakin da ake bukata da kuma boye wasu bayanai kan kisan.

Alkalin ta ce rashin kasancewar Obado a yankin Migori lokacin da aka kashe Otieno ba zai kawar da alhakinsa kan lamarin ba.

Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar masu gabatar da kara na neman a yanke wa wadanda ake zargin hukuncin kisa, haka kuma ta ki amincewa da bukatar Obado na samun hukuncin da ba zai kai shi gidan yari ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yadda Sanata Omo Agege ya tsallake rijiya ta baya a Delta

An kashe Otieno ne tsakanin ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumban 2018, bayan ta bar wani otal da ke Rongo, kudu maso yammacin Kenya, tare da wani dan jarida mai suna Barrack Oduor.

Marigayiyar ta tuntubi Oduor ne domin tattauna alakar da ke tsakaninta da tsohon gwamnan. Sai dai jim kadan bayan haka, wasu mutane suka yi awon gaba da su.

Oduor ya samu damar tserewa ta hanyar tsalle daga motar da ake tafiya da su. Bayanin da ya bayar kan yadda aka yi garkuwa da su ya taimaka matuka wajen gudanar da bincike.

Daga bisani, an gano gawar Otieno a kusa da dajin Kodera. Binciken gawarta ya nuna cewa an shake ta tare da zubar mata da jini mai yawa sakamakon raunukan wuka da aka yi mata.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa Obado ne mahaifin jaririn da Otieno ke dauke da shi a cikinta.

An samu Obado da sauran wadanda ake tuhuma da laifin kisan kai a ranar 23 ga watan Yulin 2026, bayan shafe tsawon lokaci ana shari'a.

A yayin shari'ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu 42 da kuma wasu muhimman kayayyaki da takardu 81 domin tabbatar da zarge-zargen.

Kara karanta wannan

An kashe rayuka da aka tarwatsa 'yan Obi Kwankwaso a wajen kamfen

A ranar Juma'a, kotun ta kuma ki bayar da diyya ga iyalan marigayiyar, saboda rashin isassun hujjojin da za su tabbatar da asarar kudaden da suka ce sun yi.

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.