Bincike Ya Gano Yadda Tsohon Gwamnan CBN Ya Take Umarnin Buhari wajen Canjin Kudi
- Wani jami’in ’yan sanda ya shaida wa kotu cewa Godwin Emefiele ya sauya launin takardun naira maimakon sake tsara su kamar yadda Buhari ya amince
- Shaidan ya ce bincike bai gano wata hujja da ke nuna cewa kwamitin gudanarwar CBN ya amince da sauyin launin ba
- EFCC na zargin Emefiele da sake fasalin takardun N200, N500 da N1,000 ba bisa ƙa’ida ba, da kuma buga kuɗin N684.5bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wani jami’in binciken ’yan sanda ya ba da shaida a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) a ranar Alhamis kan zargin da ake wa tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Dan sandan ya fada wa kotu cewa Emefiele ya sauya launin takardun Naira bisa ra'ayin kansa maimakon sake tsara kudin Najeriya kamar yadda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince.

Source: Getty Images
Premium Times ta ruwaito cewa Eloho Okpoziakpo, shaida ta 11 a bangaren masu gabatar da ƙara, ya bayyana hakan ne yayin bayar da shaida a shari’ar Emefiele kan zargin sake fasalin Naira ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifuffukan kuɗi.
Dan sanda ya bada shaida a kotu
Okpoziakpo, shi ne kwamishinan ’yan sanda wanda ya jagoranci binciken zarge-zargen da ake yi wa tsohon gwamnan CBN bayan cire shi daga mukaminsa a watan Yunin 2023.
Dan sandan ya bayar da shaidar ne yayin da Daraktan Masu Gabatar da Ƙara na Tarayya, Rotimi Oyedepo, SAN, ke yi masa tambayoyi.
Ya shaida wa kotu cewa masu bincike ba su gano wata hujja da ke nuna cewa kwamitin gudanarwar CBN ya gudanar da taro tare da amincewa da sauya launin takardun Naira ba.
Ya ce Emefiele ya nemi amincewar Shugaba Buhari domin sake fasalin Naira, inda ya haɗa da samfuran sababbin takardun kuɗin da aka tsara, waɗanda shugaban ƙasar ya amince da su.

Kara karanta wannan
Da gaske gwamnan Edo na da hannu a harin da aka kai wa su Kwankwaso? An samu bayani
“Amma abin da aka yi a ƙarshe ba sake fasalin takardun kuɗin ba ne kamar yadda shugaban ƙasa ya amince, sai dai sauya launinsu,” in ji Okpoziakpo.
Shari’ar na ɗaya daga cikin shari’o’i da dama da aka gurfanar da Emefiele a ciki tun bayan cire shi daga mukaminsa a watan Yunin 2023 bisa zarge-zargen rashawa da sauran laifuffukan kuɗi.
Buhari ya amince da canza launin Naira?
A zaman kotun na ranar Alhamis, Okpoziakpo ya ce Emefiele ya aika da takardar amincewar shugaban ƙasa ga Manajan Daraktan Kamfanin Buga Kuɗi da Takardun Tsaro na Najeriya (NSPM).
Sai dai manajan daraktan ya nuna damuwarsa a cikin wata wasiƙa da ya aika wa Emefiele, wadda shaidan ya karanta wa kotu.
Okpoziakpo ya ce samfuran farko da Emefiele ya miƙa wa shugaban ƙasa sun ƙunshi lambobin QR, alamomin tsaro na ruwa (watermarks) da kuma lambobi daban-daban a kan takardun N1,000, N500 da N200.

Source: Getty Images
Sai dai ya ce samfuran da Emefiele ya amince a buga daga baya ba su ƙunshi lambobin QR ba.
Shaidan ya dage cewa babu wata sabuwar amincewar shugaban ƙasa da aka samu kan takardun kuɗin da aka buga a ƙarshe.

Kara karanta wannan
Gwamna ya karɓi rahoton abubuwan da aka gano kan mutuwar matasa 37 a ofishin NSCDC
Emefiele ya musanta tuhuma 20
Kun ji cewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya musanta dukkan tuhume-tuhume 20 da aka shigar kansa a gaban kotu.
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ƙara yawan tuhume-tuhumen da take wa Emefiele, ta miƙa wa Kotu.
Asali: Legit.ng
