Bangare 1 da Bola Tinubu Ya Yi wa Atiku da Peter Obi Fintinkau a Siyasa
- Babatunde Fashola ya bayyana dalilin da ya sa Bola Tinubu ya fi Atiku da Peter Obi damar lashe zaben shugaban kasa na 2027
- Tsohon gwamnan Legas ya ce yadda Tinubu ke hada kan tsofaffin abokan hamayyarsa ya nuna kwarewarsa wajen tafiyar da Najeriya
- Fashola ya bayyana cewa Tinubu ya samu damar hada gwamnonin jihohi 30 a karkashin jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Legas - Tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola, ya bayyana yadda kwarewar Bola Tinubu ta taimaka masa a siyasa.
Fashola ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da wata babbar dama ta zarce Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2027.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan Legas ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis.
Dabarun da Tinubu ke yi a siyasa
Fashola ya ce yadda shugaban kasar ke iya rike mutanen da suka yi aiki tare da shi tare da jawo tsofaffin abokan hamayyarsa cikin tafiyarsa ta siyasa, ya ba shi fifiko kan sauran masu neman kujerar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, na daga cikin manyan masu kalubalantar Tinubu a zaben shekarar 2027.
Fashola ya ce dukkan manyan 'yan takarar shugaban kasar uku suna da alaka da shugabancin jihohi, domin sun taba zama gwamnoni ko kuma sun samu nasarar zaben kujerar gwamna a baya.
Ya bukaci masu kada kuri'a su yi nazari kan yadda mutanen da suka taba aiki da kowanne daga cikinsu suke ci gaba da kasancewa tare da su a harkokin siyasa.
A cewarsa, abin lura shi ne yadda tsoffin hadiman Tinubu suka ci gaba da kasancewa tare da shi duk da cewa ya shafe kusan shekaru 16 ba tare da rike mukamin shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura wa Atiku saƙo bayan cika shekaru 80, ya tuna halaccin da ya yi masa

Source: Facebook
Dabi'ar da ta taimaki Tinubu a siyasa
Fashola ya ce wannan dabi'a ta nuna cewa Tinubu na iya gina kyakkyawar alaka da mutane tare da rike kwararrun ma'aikata da wadanda suka taimaka masa wajen samun nasara.
Ya kuma tuna yadda Tinubu ya tsaya daram a tsohuwar jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN), wadda daga baya ta hade da wasu jam'iyyu wajen kafa APC, duk da rikice-rikice da matsin lambar siyasa.
A cewarsa, shugabancin kasa na bukatar mutum mai iya hada kan jama'a da aiki tare da kowa, musamman ganin yadda Najeriya ta kunshi al'ummomi da ra'ayoyi daban-daban.
Fashola ya ce Tinubu bai fice daga jam'iyyar APC ba lokacin da ta fuskanci matsaloli, sabanin wasu 'yan siyasa da suka bar jam'iyyun da suka taimaka musu wajen samun daukaka.
Tinubu ya fadi karfinsa a Arewa
Mun ba ku labarin cewa fadar shugaban ƙasa ta ce kamfen ɗin jam'iyyar APC a Arewa ya wargaza zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da ƙarfi a yankin.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce jam’iyyar ta nuna ƙarfin iya tara magoya baya a faɗin Najeriya.
Onanuga ya yi hasashen cewa Tinubu zai lashe zaɓen shugaban kasa da za a yi a ranar 16 ga Janairu, 2027 da gagarumin rinjaye.
Asali: Legit.ng

