Siyasar Najeriya
Kungiyar kwadago da kungiyar lauyoyin Najeriya sun nuna rashin amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa da ya yi kudin da ake biyan yan majalisa bai fi karfin aikin da suke yi ba.
Sanata Ahmed Sani Yariman-Bakura wanda tsohon Sanatan Zamfara ne, ya ce albashi da alawus din Majalisa ya yi daidai. A cewarsa, albashin Majalisa bai yi yawa ba.
Rikicin APC ta kara cabewa inda Gwamnan Edo ya sake dura kan Adams Oshiomhole. Gwamna Obaseki ya caccaki Oshiomhole ne yayin da ya gana da Jonathan.
Sanata Ahmed Sani Yariman-Bakura ya ce Gwamnan Zamfara zai koma APC. Yanzu haka dai tsohon Sanatan APC ya koma Makarantar addini bayan ya bar Majalisa.
Tsohon Gwamnan Zamfara, Ahmed Yariman Bakura ya ce mutane na rokon shi ya fito takara a 2023. Sanatan ya ce Buhari ba zai damkawa Tinubu mulki ba.
Jam’iyyar adawa ta United Progressive Party, UPP, ta dunkule tare da narkewa a cikin jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC biyo bayan soke rajistar ta da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi.
Janar Babagana Munguno ya yi wasu fallasa inda aka gane cewa Abba Kyari ya na juya akalar Gwamnatin Buhari. Me aka gano daga wadannan wasiku?
Wata Baiwar Allah ta maka Atiku kara, ta na bukatar N45m saboda ya yi amfani da hotonta wajen kamfe. Yanzu dai an daga karar har sau zuwa Ranar 22 ga Watan Afrilu.
PDP za ta dawo mulki a Jihar Imo ta Kotun koli inji Shugaban Jam’iyyar. A cewarsa Kotun koli za ta janye hukuncin da ta yi a kan zaben Gwamnan da ya ba Hope Uzodinma nasara.
Siyasar Najeriya
Samu kari