Yan Takara Sun Fara Guje Gujen Tura Sunayensu Shafin INEC saboda Tsoron Sauya Su

Yan Takara Sun Fara Guje Gujen Tura Sunayensu Shafin INEC saboda Tsoron Sauya Su

  • Jam’iyyun siyasa sun fara guje-gujen loda sunayen ‘yan takararsu zuwa tsarin INEC kafin wa’adin da aka diba ya cika
  • INEC ta ce za ta kwatanta sunayen da jam’iyyu suka loda da rahotannin masu sa ido, sannan za ta wallafa bayanan ‘yan takarar
  • ADC, PDP, LP da NDC sun bayyana kwarin gwiwar cika wa’adin INEC, yayin da APC ta ce sashen ICT ne ke ci gaba da tattara bayanansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyun siyasa sun ƙara kaimi wajen loda sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya zuwa tsarin hukumar INEC.

Hakan ya biyo bayan wa’adin ranar 11 ga Yulin shekarar 2026 da INEC ta ware domin tabbatar da bin tsari.

Yan takara sun kara kaimi wurin loda sunayensu a shafin INEC
Shugaban hukumar INEC a Najeriya, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Wasu ‘yan takara ma sun garzaya hedikwatar jam’iyyunsu domin tabbatar da cewa ba a sauya sunayensu ba, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar dan takarar gwamna a ADC miliyoyi kan fastocin siyasa a Adamawa

Lokacin karbar sunayen yan takara a INEC

A cikin sabon jadawalin zaɓe, INEC ta ce za a karɓi sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya daga 27 ga Yuni zuwa 11 ga Yulin 2026.

Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanadi cewa dole ne jam’iyyu su gabatar da bayanan ‘yan takararsu aƙalla kwanaki 120 kafin zaɓe.

Hukumar ta sanar da cewa za ta wallafa bayanan ‘yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya ranar 1 ga Agustan 2026.

Haka kuma za a fara loda bayanan ‘yan takarar gwamnoni da na majalisun jihohi daga 18 ga Yuli zuwa 8 ga Agusta.

Binciken Nigerian Tribune ya nuna cewa ‘yan takara da dama sun mamaye hedikwatocin jam’iyyunsu saboda fargabar maye gurbin sunayensu.

Wata majiya a ADC ta ce wasu sun kai takardunsu da kansu saboda rashin amincewa da jami’an jam’iyya a jihohinsu.

ADC ta magantu kan loda sunayen yan talararta a shafin INEC
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: UGC

ADC ta magantu kan suna sunayen yan takara

Sakataren yaɗa labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar ba ta da wata matsala kuma za ta cika wa’adin INEC.

Kara karanta wannan

Naja’atu: Munafuncin da ADC ta gani ta hana Ibrahim Khalil takarar gwamnan Kano

Ya ƙara da cewa da zarar INEC ta ba su lambobin shiga tsarin loda sunayen gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, za su aiwatar da aikin.

Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya ce hukumar za ta kwatanta sunayen da jam’iyyu suka loda da rahotannin masu sa ido a zaɓukan fidda gwani.

Ya ce tsarin ba zai karɓi sunayen da ba su dace da sakamakon zaɓukan fitar da gwani ba, cewar Punch.

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyu na da damar maye gurbin ‘yan takara idan Dokar Zaɓe ta ba da dama.

Jam’iyyun LP da PDP sun ce sun kusan kammala aikin, inda LP ta bayyana cewa ta loda sama da kashi 90 cikin 100 na sunayen ‘yan takararta, yayin da PDP ta ce ta kammala kashi 100 cikin 100 ba tare da wata matsala ba.

Jam’iyyar NDC ma ta bayyana cewa za ta cika wa’adin duk da shari’ar da ake yi kan rajistarta.

Loda sunayen yan takara: INEC ta kara wa'adi

Mun ba ku labarin cewa hukumar INEC ta ɗaga ranar bai wa jam'iyyun siyasa lambar shiga manhajar gabatar da sunayen 'yan takara.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na barazana a iyakokin Najeriya, sojoji sun shirya murkushe su

INEC ta ce an yi jinkirin ne domin tabbatar da cewa aikin loda takardun tsayar da 'yan takara na zaɓen 2027 zai gudana cikin sauƙi.

PDP ta riga ta bai wa 'yan takararta takardun shaidar nasara da fom na INEC, tare da umarnin mayar da su cikin sa'o'i 72.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.