PDP ta nemi a sake duba hukuncin kotun koli kan zaben Buhari

PDP ta nemi a sake duba hukuncin kotun koli kan zaben Buhari

- PDP ta yi kira ga sake duba hukuncin kotun koli kan zaben Buhari da Atiku

- A shekarar bara ne kotun kolin ta yi watsi da karar da aka shigar kan zaben Buhari

- Tsohuwar jam’iyyar mai mulki ta yi zargin cewa APC na lalata damokradiyar kasar

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta nemi a sake duba hukuncin kotun koli wacce ta tabbatar da zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben Shugaban kasa na 2019.

Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyar a wasu jerin rubutu da ta wallafa a safinta a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, ta ce tana neman hakan ne biyo bayan bukatar da jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ta shigar na sake duba hukuncinta a jihohin Zamfara da Bayelsa.

PDP ta nemi a sake duba hukuncin kotun koli kan zaben Buhari
PDP ta nemi a sake duba hukuncin kotun koli kan zaben Buhari
Asali: Facebook

Jam’iyyar ta kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki ta lalata damokradiyyar kasar da aka sha fama wajen ginawa, inda ta kara da cewa lokaci ya zo da dukkanin yan Najeriya za su kasance a hade domin kare kasar da kuma kareta daga mamayar siyasa da azzaluman mutane.

Kakakin jam’iyyar ta PDP, Kola Ologbodiyan ya zargi jam’iyyar mai mulki da kokarin razana alkalan kotun.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: Mutane 5 sun mutu yayinda zanga-zangar Sagamu ya munana

Ologbodiyan ya ce jam’iyyar PDP za ta kuma bukaci sake duba hukuncin kotun koli kan jihohin Osun, Kano, Katsina da Kaduna.

A wani labarin kuma, mun ji cewa darekta Janar na kungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC, PGF, Salihu Lukman, ya bayyana cewa APC ta tashi daga jam’iyyar siyasa a karkashin shugabanta Adams Oshiomhole.

Salihu Lukman ya ke cewa babu wani bangare na jam’iyyar APC ya ke zama kamar yadda doka da tsarin jam’iyyar su ka bayyana, kusan ma dai jam’iyyar ta rasa kan ‘Ya ‘yanta.

Mista Salihu Lukman ya ce daga cikin abubuwan da su ka jawo matsala a tafiyar APC su ne yadda ake tsaida ‘Yan takara, inda jam’iyyar ta ke bada tikitinta ga wanda ta ga dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel