Gombe: APC na Shirin Janye Manyan PDP don Kifar da Pantami, Ta Ziyarci Bayero

Gombe: APC na Shirin Janye Manyan PDP don Kifar da Pantami, Ta Ziyarci Bayero

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya da Jamilu Gwamna sun kai ziyara gidan Sanata Usman Bayero Nafada na jam'iyyar PDP a Gombe
  • Ziyarar ta zo ne a ranar Lahadi yayin da Sheikh Isa Ali Pantami na PDP ma ke tara mabiyansa don tattauna lamuran siyasar jihar
  • Mazauna jihar sun yi sharhi kan ziyarar tare da bayyana ra'ayoyi daban-daban game da makomar siyasar Gombe kafin babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe - Dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar APC a zaben 2027, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna ya gana da tsohon Sanata Usman Bayero Nafada, wanda yake ɗan PDP ne.

Wannan ziyara ta faru ne a ranar Lahadi, 12 ga Yuli 2026, inda Gwamna ya samu rakiyar gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, shugaban APC na kasa da Alhaji Yunusa Yakubu.

Kara karanta wannan

Yan sandan jihohi: Barau Jibrin ya fadi amfanin shirin ga Arewacin Najeriya

Bayero Nafada, Inuwa Yahaya shugaban APC da Jamilu Gwamna
Manyan APC a Gombe da Najeriya da suka hallara gidan Bayero Nafada. Hoto: Dr Jamil Gwamna.
Source: Facebook

Jamilu Gwamna ya wallafa a Facebook cewa tattaunawarsu ta ta'allaka ne kan haɗin kai, mutunta juna, da kawo cigaba a jihar Gombe gaba ɗaya.

Ziyarar ta dauki hankalin jama'a

Abin da ya sa ziyarar ta dauki hankali shi ne cewa Sanata Nafada jigo ne a PDP, wanda a baya ya tsaya takarar gwamna a jihar Gombe amma bai ci nasara ba.

Ganin shugabannin APC sun je gidansa yana ɗauke da saƙon neman haɗin kai, domin samawa jam'iyyar nasara a zaben 2027 da ke tafe.

Bugu da ƙari, wannan ziyara ta zo ne a lokacin da Sheikh Isa Ali Pantami na PDP ma yake gudanar da taronsa na karɓar mutane a lungu da sako na jihar, wanda hakan ya ƙara zafi a tattaunawar siyasar Gombe kafin 2027.

Martanin jama'a kan ziyarar

Mazauna jihar sun bayyana ra'ayoyi iri-iri game da ziyarar a karkashin sakon da Dr Jamilu Gwamna ya wallafa a shafinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya garzaya wurin Kashim Shettima bayan Tinubu ya zaɓi abokin takara a 2027

Sarkin Yakin Ajin Hadda ya rubuta cewa:

"Gaisheka gwamna mai jiran gado "

A daya bagaren kuma, Khaleel Ahmad Bappah ya ce:

"Lissafi ya kwace an fara debo kara da kiyashi don nuna babu matsala. Yo in irin wadannan din ne a taro dubu ma ba abin da za su yiwa tafiyar Pantami da al'ummar jihar Gombe lungu da sako suka karbe ta hannu biyu."
Bayero Nafada, Inuwa Yahaya da shugaban APC
Shugaban APC a tsakiyar Inuwa Yahaya da Bayero Nafada. Hoto: Dr. Jamil Gwamna
Source: Facebook

Shamsu Yarima Dokaji ya rubuta cewa:

"Allah ya kara albarka cikin wannan tafiya mai tarin albarka."

Damak N Bala kuwa ya ce:

"Gombe ta Malam Isa Ali pantami ce insha Allah"

A sanarwar da ya fitar, Jamilu Gwamna ya kara da cewa irin taron yana ƙarfafa hadin kan al'umma da kokarin kawo cigaba ga jama'ar Gombe.

An hango nasarar Pantami

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani malamin jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dr Kabiru Danladi Lawanti ya yi hasashe kan siyasar jihar Gombe.

Kara karanta wannan

'Sai Arewa ta yi tsayin daka': Inuwa Yahaya ya zaburar da gwamnoni a Kaduna

Ya bayyana cewa har yanzu akwai alamun cewa dan takarar PDP, Sheikh Isa Ali Pantami na da damar da zai lashe zaben gwamna a Gombe.

Dr Lawanti ya gina hasashen ne da cewa Pantami ya samu karɓuwa a wajen jama'ar Gombe, tasirin ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu abubuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng