Yariman-Bakura; Jama’a su na kiran in yi takarar Shugaban kasa, kuma zan fito

Yariman-Bakura; Jama’a su na kiran in yi takarar Shugaban kasa, kuma zan fito

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura, ya bayyana cewa zai fito takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Ahmed Sani Yariman Bakura ya ke cewa duk da shi ‘Dan Arewa ne zai tsaya takarar shugaban kasa, tun da shi ‘Dan Najeriya ne domin bai yadda da siyasar bangaranci ba.

Sanata Ahmad Yariman Bakura wanda ya yi aikin gwamnati, ya kuma yi gwamna daga 1999 zuwa 2007, kafin ya zama Sanata, ya ce kowa ya na da damar ya mulki Najeriya.

A hirarsa da ya yi wa Daily Trust da ta fito a Ranar Lahadi, ya ce: “Mutane sun fara samu na domin yi mani kamfen din shugaban kasa. Jama’a su na roko na in fito takara. a 2023”

A cewarsa, Muhammadu Buhari ba zai mikawa Asiwaju Bola Tinubu ragamar APC ba, inda ya ce ko da akwai wata yarjejeniya a tsakaninsu, ba za ta yi aiki a zabe mai zuwa ba.

KU KARANTA: Atiku ya yi magana bayan Boko Haram sun shiga Adamawa

Yariman-Bakura; Jama’a su na kira na in fito takarar Shugaban kasa, kuma zan fito
Ahmed Yariman-Bakura ya ce bai da N20m a lokacin da ya ci zaben Gwamna
Asali: UGC

“Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa ta hanyar zaben kato-bayan-kato za a tsaida ‘Dan takarar shugaban kasa, don haka babu yadda za ayi ya ce kowa sai ya zabi Bola Tinubu.”

“Na fada maku, Buhari ya riga ya fadi abin da ke ransa, ya ce bai da wani ‘Dan takara kuma ka da wani ya yi amfani da sunansa. Ya riga ya fadi wannan.” Inji Ahmed Yarima.

Tsohon gwamnan kasar ya ke cewa zabe za ayi na adalci domin fito da wanda zai rikewa jam’iyyar APC tuta a zaben shugaban kasa mai zuwa, don haka ya ce zai jarraba sa’arsa.

‘Dan siyasar ya na ganin cewa ya na da abin da ake bukata na mulkin kasar, ko da cewa bai da kudi irin na Bola Tinubu, ya ce ba dole sai da dinbin dukiya ake lashe zabe ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://twitter.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng