APC NWC: Shugaban PGF ya yi tir da rawar Shugabancin Oshiomhole

APC NWC: Shugaban PGF ya yi tir da rawar Shugabancin Oshiomhole

Darekta Janar na kungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC, PGF, Salihu Lukman, ya bayyana cewa APC ta tashi daga jam’iyyar siyasa a karkashin shugabanta Adams Oshiomhole.

Salihu Lukman ya ke cewa babu wani bangare na jam’iyyar APC ya ke zama kamar yadda doka da tsarin jam’iyyar su ka bayyana, kusan ma dai jam’iyyar ta rasa kan ‘Ya ‘yanta.

“Za a iya gardama game da ko har yanzu akwai rajitsa da ke kunshe da ainihin ‘Ya ‘yan jam’iyyar a yau. Idan an ci sa’a shi ne ace rajitsar ‘Ya ‘yan jam’iyya na 2015 ta na nan.”

Lukman a wata doguwar takarda da ya rubuta, ya ce Kwamred Adams Oshiomhole ya na aikin ‘Dan Sanda, Lauya da kuma Alkali, duk shi kadai a jam’iyyar ta APC mai mulki.

Jaridar Vanguard ta rahoto Salihu Lukman ya na yin wannan jawabi. Ko da Jaridar ta nemi jin ta bakin Kwamred Adams Oshiomhole, bai iya daukar waya ko amsa sakonni ba.

KU KARANTA: Oshiomhole ya yi kadan ya hana in zarce a kan mulki - Obaseki

APC NWC: Shugaban PGF ya yi tir da rawar Shugabancin Oshiomhole
Wasu na kira a tsige Shugaban jam’iyyar APC Oshiomhole
Asali: UGC

“Maganar gaskiya ita ce a halin da ake ciki yau, APC ba ta aiki a matsayin jam’iyyar siyasa.”

Mista Salihu Lukman daga cikin abubuwan da su ka jawo matsala a tafiyar APC su ne yadda ake tsaida ‘Yan takara, inda jam’iyyar ta ke bada tikitinta ga wanda ta ga dama.

A cewar Darektan na kungiyar PGF, an kawo matsala game da yadda ake sasanta rigimar cikin gida, Lukman ya ce shugaban jam’iyya ne ya ke ruwa da tsaki a sha’anin sulhu.

“Rigimar jam’iyyar ya na kara cabewa ne a kullum. Yanzu abin ya kai ba a ganin cewa Adams Oshiomhole da majalisarsa za su iya shugabantar jam’iyyar ga ci.” Inji Lukman.

Haka zalika Lukman ya na ganin cewa matsalar shugabanci ta sa APC ta rasa nasarar da ta samu a zaben jihar Zamfara da Bayelsa don haka ya ke ganin sai APC ta yi da gaske.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel