Adams Oshiomhole ya na yin abin da ya ga dama da gadara inji Godwin Obaseki

Adams Oshiomhole ya na yin abin da ya ga dama da gadara inji Godwin Obaseki

A Ranar Lahadi, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya zargi tsohon Mai gidansa wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, da yin abubuwan da ya ga dama.

Mai girma Godwin Obaseki ya bayyana cewa Adams Oshiomhole ya na abubuwansa da gadara, ganin cewa ya ziyarci Edo ba tare da ya sanar da gwamnati game da zuwansa ba.

Gwamnan ya shaidawa ‘Yan jarida wannan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya kawo masa ziyara ta musamman har gida.

Godwin Obaseki ya ce idan har da mutunci, ya kamata ace tsohon gwamna Adama Oshiomhole ya sanar da gwamnatin jihar Edo cewa zai shigo jihar, ba kawai ya zo kwatsam ba.

A game da ziyarar tsohon shugaban kasar, gwamnan ya ke cewa ziyara ce kurum ta kawo shi. Obaseki ya kuma bayyana cewa sai da Jonathan ya sanar da shi game da zuwansa.

KU KARANTA: Yadda 'Yan siyasa ke jawo matsalar rashin tsaro - Tsohon Gwamna

Adams Oshiomhole ya na abubuwan da ya ga dama da gadara inji Obaseki
Obaseki ya caccaki Oshiomhole yayin da ya gana da Jonathan
Asali: UGC

“Ziyara ce ta kawo tsohon shugaban kasa, a matsayinsa na wanda ya rike babban mukami, kun ji abin da ya dace. Sanin mutunci ne ka sanar da mutum idan za ka kawo masa ziyara.”

“Akasin abin takaicin da mu ke samu a jihar Edo. Abin bakin ciki ne mutumin da ya yi gwamna ya rika shigowa jiha ba tare da ya san ya rubutawa gwamnati game da zuwansa ba.”

Obaseki ya ce a matsayinsa na Gwamna kuma Mai kula da harkar tsaro a jiharsa, ya kamata ya san cewa Oshiomhole zai shigo jihar, ba kurum ya saba doka don ya na jin ya isa ba.

Ziyarar Jonathan ta zo a lokacin da ake ta faman rigima tsakanin Obaseki da shugaban APC na kasa. Dama can ana rade-radin gwamnan ya na shirin sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel