Atiku Ya Fadi Abin da Tinubu Ya Kamata Ya Yi bayan Ceto Dalibai 44 a Oyo
- 'Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya yaba wa sojoji da jami'an tsaro kan ceto dalibai da malamai 44 da aka sace a jihar Oyo
- Sai dai ya caccaki shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu game da abin da ya kira rashin iya shugabanci da nuna jagoranci a kasar nan
- Atiku ya bukaci gwamnati ta ci gaba da matsa lamba kan 'yan bindiga har sai an kubutar da duk wadanda ke hannunsu a sassa daban-daban na kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soi shugaban kasar Bola Tinubu.
Ya bayyana takaici a kan matakin da Bola Ahmed Tinubu ya dauka bayan ceto dalibai 44 da aka sace a jihar Oyo a matsayin gazawar shugabanci.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Atiku ya ce duk da cewa aikin ceton ya cancanci yabo, shugaban kasar ya rasa wata muhimmiyar dama ta nuna jagoranci ta hanyar bayyana wa al'umma yadda aka gudanar da aikin.
Atiku ya yabi jami'an tsaro
Jaridar Leadership ta wallafa cewa a ranar Juma'a 10 ga watan Yuli, 2026, rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa hadin gwiwar da ta yi da hukumomin leken asiri da sauran jami'an tsaro sun ceto dalibai da malamai 44 da aka sace a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo a watan Mayu 2026.
Amma a martaninsa ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Asabar, 11 ga watan Yuli, 2026, Atiku ya yaba da nasarar aikin tare da jinjinawa sojoji da sauran jami'an tsaro.
Ya ce:
"Kubutar da wadannan yara da ba su yi laifin komai ba daga hannun 'yan ta'adda nasara ce ga jaruman sojojinmu kuma abin farin ciki ne ga kowane 'dan Najeriya. Sun cancanci godiyar al'umma."
Atiku ya soki Tinubu kan tsaro
Atiku ya ce sojojin sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu amma fadar shugaban kasa ba ta nuna irin jagorancin da ake bukata ba.

Source: Twitter
Ya ce matsalar ta'addanci tana addabar kasashe da dama, amma abin da ke bambanta gwamnati mai nagarta da wacce ba ta da kishi shi ne yadda shugabanni ke mayar da martani idan jami'an tsaro suka samu irin wannan gagarumar nasara.
A cewarsa:
"Abin da 'yan Najeriya suka yi tsammani shi ne ganin Babban Kwamandan Rundunar Soji yana a kan gaba."
Ya kara da cewa bayan nasarar aikin ceton, ya dace shugaban kasa ya fito tare da shugabannin hukumomin tsaro domin ya sanar da al'umma yadda aka gudanar da aikin.
Sannan ya kamata ya yabawa sojojin, ya kwantar wa iyalan wadanda har yanzu ke hannun masu garkuwa hankali, tare da isar da sako mai karfi ga 'yan bindiga da 'yan ta'adda cewa gwamnatin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba.

Kara karanta wannan
'Abin da Tinubu ya kamata ya yi wa Gbajabiamila kafin binciken ICPC': Hadimin Atiku
Atiku ya gargadi gwamnatin Tinubu
A baya, mun wallafa cewa 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC Atiku Abubakar ya gargadi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da jagorori a jam'iyyun adawa, Peter Obi da Nasir El-Rufa'i.
Ya bayyana haka ne a yayin da 'dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya yi ikirarin ana neman rayuwarsa, kuma ba lallai ya kai babban zaben 2027 saboda zargin ana neman rayuwarsa.
Haka kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i na garkame a hannun hukumar yaki da rashawa ta ICPC yayin da iyalansa ke kukan an haramta masa ganin likita tare da kama wanda ke kula da lafiyarsa.
Asali: Legit.ng

