Gwamnan Bauchi ya dakatar da shugaban karamar hukuma
- Gwamnan Bauchi Bala Mohammad ya amince da dakatar da Alhaji Baffa Bara, Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Kirfi
- Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mista Muktar Gidado, babban mai ba gwamnan shawara kan kafofin watsa labarai
- Gidado ya ce dakatarwar za ta fara aiki ne a nan take
Gwamna Bala Mohammad na jahar Bauchi ya amince da dakatar da Alhaji Baffa Bara, Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Kirfi.
Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mista Muktar Gidado, babban mai ba gwamnan shawara kan kafofin watsa labarai a Bauchi a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu.
Gidado ya dakatarwar zai fara aiki ne a nan take.

Asali: Twitter
“Gwamna Bala Mohammad ya amince da dakatar da Alhaji Baffa Bara, Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Kirfi.
“Dakatarwar ya kasance saboda dabi’unsa wajen tafiyar da harkokin karamar hukumar da kuma wasu lamura da suke shafi badakalar kudi wanda ya ja hukumar EFCC ta gayyace shi wanda gwamnatin jahar ke kallo a matsayin cin mutunci da ba za ta iya lamunta ba.
DUBA WANNAN: Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari
“Gwamnati ya kuma lura cewa dakataccen Shugaban karamar hukumar baya zantawa da masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar kamar yadda gwamnan jahar ya yi umurni.
“Wannan hali ya saba tsarin wakilci da damokradiyya kamar yadda gwamnati mai ci a jahar ta tsara,” in ji Gidado.
An umurci dakataccen Shugaban da ya mika ragamar mulki ga mataimakin Shugaban karamar hukumar tare da dukkanin kayan gwamnati da ke a hannunsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng