Siyasar riga yanci: Wata babbar jam’iyyar adawa ta narke a cikin jam’iyyar APC

Siyasar riga yanci: Wata babbar jam’iyyar adawa ta narke a cikin jam’iyyar APC

Jam’iyyar adawa ta United Progressive Party, UPP, ta dunkule tare da narkewa a cikin jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC biyo bayan soke rajistar ta da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi.

Daily Trust ta ruwaito jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne a taron shuwagabannin jam’iyyar da kwamitin amintattun jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki daya gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Rikicin ma’aurata: Lebura ya kashe matarsa da mugun duka a jahar Legas

Siyasar riga yanci: Wata babbar jam’iyyar adawa ta narke a cikin jam’iyyar APC
Jam’iyyar UPP ta dunkule da jam’iyyar APC tun daga sama har kasa
Asali: Facebook

A yayin taron, shuwagabannin jam’iyyar sun bayyana cewa sun dunkule cikin jam’iyyar APC tun daga sama har kasa, ma’ana tun daga matakin mazaba, zuwa matakin karamar hukuma, matakin jaha da kuma matakin tarayya.

Shugaban jam’iyyar, Chekwas Okorie ne ya bayyana haka cikin sanarwar bayan taro da raba ma manema labaru, inda yace taron ya umarci dukkanin mambobin jam’iyyar UPP su yi rajista da jam’iyyar APC, sa’annan yace babu bukatar su kalubalanci matakin da INEC ta dauka a kansu a gaban kotu.

“Mun yi nazari tare da yin duba da zabin da muke dasu, daga ciki har da gayyatar da wasu jam’iyyun da suka tsallake tantancewar hukumar zabe INEC suka yi mana na hadewa, amma bayan duba cewa a ranar 17 ga watan Agustan 2018 jam’iyyarmu ta sanar da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

“Wanda a wannan lokaci muka umarci yayan jam’iyyarmu su taya dan takarar shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar APC, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe, kuma mambobinmu suka yi biyayya ga wannan umarni ba tare da nuna tirjiya ba.

“Sa’annan tare da duba da halin da muke ciki a yanzu, jam’iyyarmu ta yanke hukuncin abin da ya fi dacewa shi ne mu narkar da jam’iyyarmu cikin jam’iyyar APC tun daga mazaba har tarayya.” Inji shi.

Daga karshe shugaban UPP, Okorie ya ce jam’iyyar APC ta basu tabbacin tarbarsu cikin mutunci da aminci, kuma za ta basu dama kamar yadda kowanne dan jam’iyyar yake da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel