An Kwarfe Atiku, Nafiu Bala Ya Sa Sunayen 'Yan Takarar ADC a Shafin INEC

An Kwarfe Atiku, Nafiu Bala Ya Sa Sunayen 'Yan Takarar ADC a Shafin INEC

  • Tsagin jam'iyyar ADC na Nafiu Bala ya kammala daura sunayen 'yan takarararta a shafin INEC don zaben 2027
  • Farfesa Chris Uba daga jihar Anambra ne aka zaba a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a bangaren Nafiu
  • Haka kuma, Dr. Shamsuddin Modibbo Barkindo dan jihar Adamawa ne aka zaba a matsayin mataimakin dan takarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Tsagin jam'iyyar ADC, ta sanar da kammala shigar da sunayen 'yan takarararta na zaben shekarar 2027 a tashar INEC, hukumar zaben kasa.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da zuwa kotu domin shari'a a jam'iyyar tsakanin bangaren Nafiu Bala da David Mark.

Nafiu Bala Gombe
Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala a wajen taro. Hoto: Nafiu Bala
Source: Facebook

A cikin sanarwar da Nafiu Bala Gombe ya fitar a Facebook a ranar Lahadi, 12 ga Yuli 2026, ya bayyana cewa an sanya sunayen 'yan takara a hukumance, ciki har da dan takarar shugaban kasa, mataimakin dan takarar, da 'yan takarar majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi abin da Tinubu ya kamata ya yi bayan ceto dalibai 44 a Oyo

Dan takarar ADC da aka tsayar

Farfesa Chris Uba, wanda ya kai shekara 71 da ADC ta tsayar, dan jihar Anambra ne, kuma ya yi karatu a jami'ar Nsuka da kuma a Birtaniya.

Shi ne ADC ta zaba a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa. Mataimakinsa kuma shi ne Dr. Shamsuddin Modibbo Barkindo, dan jihar Adamawa mai shekara 65, wanda ya halarci jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Nafiu Bala Gombe ya bayyana a sanarwarsa cewa wannan nasarar tana nuna tsayuwar jam'iyyar kan manufofinta na tabbatar da dimokuradiyya da kare hakkin mambobin jam'iyyar wadanda suka kafa ta da kuma suka raya ta.

Wannan labari ya zo ne a lokacin da aka samu rahotannin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kasance daga cikin 'yan takarar da wani bangare na ADC ya goyi bayansu.

Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O Ibe
Source: Facebook

An taya 'yan ADC murna

Bayan sanarwar, hadimin shugaban tsagin ADC, Hon. Aliyu Bala Shinkafi, ya fitar da wata sanarwa ta murna yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Shettima ya kai wa Tinubu ziyara bayan APC ta tabbatar da shi a tikitin 2027

"Ina miƙa saƙon taya murna ga dukkan halastattun 'yan Jam'iyyar ADC mai albarka ƙarƙashin jagorancin Hon. Nafi'u Bala Gombe, halastaccen shugaban Jam'iyyar na Ƙasa.
A yau, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da Chiris Uba a matsayin halastaccen ɗan takarar jam'iyyar ADC a zaɓen shekarar 2027. Wannan babban ci gaba ne ga jam'iyyarmu."

Sanarwar ta dauki hankali a shafukan sada zumunta, inda wasu mutane sun nuna goyon bayansu ga wannan matakin da jam'iyyar ta dauka yayin da wasu kuma suka rika korafi.

Ana so Atiku ya hakura

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff ya yi kira ga Atiku Abubakkar da ya hakura da takara a 2027.

Ali Modu Sheriff ya bayyana haka ne yayin da lamuran siyasa ke kara daukar hankali a Najeriya, musamman kan Atiku da Bola Tinubu.

Tsohon gwamnan ya ce ya kamata Bola Tinubu ya karasa wa'adi na biyu kafin daga bisani Atiku Abubakar ya fito neman shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng