Siyasar Kano: Abba Kabir Ya Dauki Mataimakin Gwamna a Takarar 2027

Siyasar Kano: Abba Kabir Ya Dauki Mataimakin Gwamna a Takarar 2027

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya sanar da cewa zai ci gaba da aiki da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa a zaben 2027
  • Sanarwar hakan ta fito ne bayan taron da aka yi a Abuja tare da jami'an gwamnatin tarayya masu aiki tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • A bayanin da ya yi, gwamnan ya yaba wa Garo saboda amincin da ya nuna da kuma gudummawar da ya bayar tun da ya fara aiki tare da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya yanke shawarar ci gaba da tafiya da mataimakinsa, Murtala Garo, a matsayin abokin takarar sa a zaben gwamna da za a gudanar a shekarar 2027.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne tabbatar da matakin Abba Kabir Yusuf a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya garzaya wurin Kashim Shettima bayan Tinubu ya zaɓi abokin takara a 2027

Abba Kabir Yusuf da Murtala Sule Garo
Murtala Garo na gaisawa da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sanusi Bature ya wallafa a Facebook cewa an yanke shawar ne a wani taro na musamman da aka gudanar a gidan shakatawa na Gwamnan Kano da ke birnin Abuja.

Dalilin Abba na zaben Garo

A cewar Abba Kabir Yusuf, shawarar da ya yanke ta kasance sakamakon sadaukarwa da aminci da Murtala Garo ya nuna tun bayan da ya karbi mulkin mataimakin gwamna.

Gwamnan ya ce dangantakar aiki da ke tsakaninsu ta kasance mai kyau, inda ya kira Garo a matsayin abokin aiki na gari kuma kwararre.

"Ban taba nadamar zabar Garo a matsayin mataimakin gwamna a wadannan watanni da suka wuce ba, kuma ya nuna cewa zabin da na yi daidai ne. Ina son a tabbatar muku cewa na aminta da shi,"

In ji Abba Yusuf.

Gwamnan ya kara da cewa tallafin da Garo ya ba wa gwamnatinsu ya karfafa kokarin da suke yi wajen aiwatar da shirin raya jihar Kano da cika alkawaruruka da aka yi wa jama'a.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi dabara, an gano hikimar ci gaba da tafiya da Kashim Shettima

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir a ofis. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Kiran haɗin kan jam'iyya

Bayan sanar da sunan abokin takararsa, Gwamna Abba Yusuf ya jaddada muhimmancin hadin kan jami'an jam'iyya da masu goyon bayan gwamnati a shirin zaben 2027.

Ya yi kira ga dukkan shugabannin jam'iyya da masu aiki a gwamnatin tarayya da su kasance a matsayin tsintsiya madaurinki daya, yana mai cewa nasarar da gwamnatinsa za ta samu tana bukatar goyon bayan kowa.

"Dole ne mu kasance masu maida hankali, mu kasance daya kuma mu nuna sadaukarwa, kuma mu shirya fuskantar kalubalen da ke gaba,"

In ji gwamnan.

Abba ya yi kira ga lauyoyi

A wani labarin, mun kawo muku cewa Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga lauyoyi game taka muhimmiyar rawa a zaben 2027 da za a yi a gaba.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taron lauyoyi da ya halarta kan yadda za a cigaba da farfado da lamura a Kano da Najeriya.

Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa kamar sauran kwararu, lauyoyi na da muhimmiyar rawar da za su taka a lokutan zaben 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng