Zargin N6.3b: EFCC ta maida Jonah Jang da Ma’ajin Gwamnati gaban Alkali

Zargin N6.3b: EFCC ta maida Jonah Jang da Ma’ajin Gwamnati gaban Alkali

A jiya Ranar Litinin, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa, ta kuma gurfanar da tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Jonah Jang a kotu.

Hukumar dillacin labarai ta ce EFCC ta gurfanar da Jonah Jang ne tare da wani Ma’ajin ofishin Sakataren gwamnatin jihar, Yusuf Pam, bisa zargin satar Naira biliyan 6.3.

A shekarar 2018 ne EFCC ta fara shigar da karar Jonah Jang da Yusuf Pam a kotu, inda ta zarge su da laifuffuka 17 wadanda su ka hada da karkatar da dukiyar gwamnati.

EFCC ta zargi tsohon gwamnan da ma’aikacin gwamnatin Filaton da rashin gaskiya da kuma cin amanar da aka damka masu, wanda tuni ake wankesu daga duk zargin.

Yanzu EFCC ta sake gabatar da wannan kara a gaban babban Alkalin jihar Filato, Yakubu Dakwak. Mai shari’a Dakwak ya maida shari’ar a hannun Christy Dabup.

KU KARANTA: Alkalin kotu ta wanke Sanata Ike Ekweremadu daga zargi

Zargin N6.3b: EFCC ta maida Jonah Jang da Ma’ajin Gwamnati gaban Alkali
EFCC ta na zargin Jonah Jang da sace N6b a lokacin ya na Gwamna
Asali: Depositphotos

A.O. Otolade wanda shi ne babban Lauyan EFCC da ke tuhumar Jonah Jang da Pam, ya sake gabatar da zargin da ake yi wa wadannan mutane a gaban kotu a zaman jiya.

Bayan A. O. Otolade ya karanto wadannan zargi da EFCC ta ke da su, wadanda ake tuhumar sun amsa cewa ba su aikata laifuffukan da hukumar ta ke zarginsu da su ba.

Lauyan tsohon gwamnan, Edward Pwajok, SAN ya bukaci Alkali ya bada belin wadanda ake kara bisa sharudan da aka taba ba su a lokacin da aka saurari shari’ar a 2018.

Shi ma Barista Sunday Odeh wanda ya ke kare Pam, ya goyi bayan rokon da Lauya Pwajok ya yi. Lauyan da ya tsayawa EFCC bai nuna adawarsa ga wannan bukata ba.

A karshe Alkali Christy Dabup ta gamsu da wannan roko, ta bada belin wadanda ake tuhuma bisa sharadi. Dabup ta dakatar da karar har sai Ranar 26 da 27 ga Watan Mayu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel