Dan Takarar Shugaban Kasa da zai ba da Ilimi Kyauta, a Rika ba Dalibai Abinci

Dan Takarar Shugaban Kasa da zai ba da Ilimi Kyauta, a Rika ba Dalibai Abinci

  • Mai rajin kare hakkin bil adama, Omoyele Sowore ya fitar da tsarin ilmi na jam'iyyarsa ta AAC yayin da ake shirin zaben 2027
  • Sowore ya yi alkawarin cewa ilimi zai zama kyauta daga makarantar firamare har jami'a, kuma ba za a biya kudin WAEC ko NECO ba
  • Takardar manufofinda ya fitar ta kunshi matakai 20 da suka shafi abubuwan more rayuwa, fasaha, malamai da walwalar dalibai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa jam'iyyar AAC a zaben 2027, Omoyele Sowore ya gabatar da tsarin manufofin ilimi na jam'iyyarsa ga jama'a.

Sowore ya fitar da manufofinsa, inda ya bayyana cewa idan ya hau mulki, ba za a bukaci dalibi ya biya kudin WAEC, NECO ko wata jarrabawa ta gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar wa 'yan Najeriya hankali, ya yi alkawarin romon dimukradiyya

Mai neman shugaban kasa, Omoyele Sowore
Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da ya ce zai inganta ilimi. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, Sowore ya ce iliimi zai zama kyauta daga farkon karatu har kammala jami'a, tare da dakunan karatu na zamani, albashi mai kyau ga malamai, tallafin karatu ga dalibai da sauransu.

Me tsarin Sowore ya kunsa?

Takardar manufofin ta kunshi matakai 20 da suka shafi damar samun ilmi, abubuwan more rayuwa, kudi, manhaja, fasaha, bincike da walwalar dalibai.

A bangaren tsarin karatu, Sowore ya ce zai kawo sauye-sauye a tsarin makaranta ta hanyar kawo shekaru biyar na firamare, biyar na sakandare da kuma shekaru hudu na jami'a.

Punch ta wallafa cewa ya kuma alkawarta kafa kwaleji a kowace karamar hukuma da za ta ba da takardar shaidar karatu ta shekaru biyu.

Game da tallafin dalibai, manufofin sun nuna cewa dalibin jami'ar gwamnati zai samu tallafi kowane zangon karatu don taimaka masa a harkar karatu da rayuwarsa ta yau da kullum.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Sowore ya kuma yi alkawarin sauya duk kwalejojin kimiyya da fasaha zuwa jami'o'i, da kuma kare 'yancin ƙungiyoyin dalibai a makarantu.

Batun inganta malaman makaranta

A bangaren malamai, tsarin ya nuna za a inganta albashinsu, a ba su gidaje da damar bincike da kuma karin kyautata masu. An kuma alƙawarta kafa cibiyoyin horar da malamai na tsawon shekaru biyu.

Dan takarar AAC, Omoyele Sowore
Omoyele Sowore a kotu yayin shari'a. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Getty Images

Takardar ta kuma yi alkawarin tallafin bincike a fannonin magunguna, makamashi, fasahar AI da bangaren lafiyar al'umma.

A bangaren kulawa da dalibai, tsarin ya kama ba da abinci na yau da kullum, kula da kiwon lafiya, tallafi ga wadanda ke da bukata ta musamman.

Sowore ya nuna cewa tsarin nasa ba alkawarin siyasa ba ne, sai dai alkawari na gaske na gina kasa inda talauci ba zai hana yaro samun ilmi ba.

An kara kudin NECO

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara kudin da dalibai za su rika biya kafin rubuta jarrabawar NECO.

Rahotanni sun nuna cewa za a kara kudin ne da sama da kaso 80, inda za a dawo biyan N50,000 alhali abin da ake biya a baya bai kai N30,000 ba.

'Yan Najeriya da dama sun yi korafi kan karin kudin, wasu na cewa lamarin zai kara yawan yaran da ba su zuwa makaranta a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng