An Cafke Mata da Yaran 'Yan bindiga, an Saki Bidiyo bayan Sace Daliban Oyo

An Cafke Mata da Yaran 'Yan bindiga, an Saki Bidiyo bayan Sace Daliban Oyo

  • Labarin ya fito kan yadda jami'an DSS suka kama mata da 'ya'yan 'yan bindigan da suka yi garkuwa da dalibai 39 da malamai 7 a Oyo
  • Bidiyon iyalan 'yan ta'addan da aka fitar ya ja hankalin 'yan bindigan, ya sa suka yi watsi da matsayarsu ta farko kan sakin daliban
  • Rahoto ya nuna cewa sojojin sun kashe 'yan bindiga da dama, sun kama wasu takwas, sun ceto dukkan malamai da daliban da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ibadan - An samu sababbin bayanai game da yadda aka yi nasarar ceto dalibai 39 da malamai da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Oyo.

Ranar 15 ga watan Mayu 2026, maharan suka sace yara da malamai daga al'ummomin Ahoro-Esinle, Yawota da Alawusa da ke Karamar Hukumar Oriire a Oyo.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka kutsa dajin Oyo, suka gwabza da 'yan bindiga yayin ceto dalibai

Daliban da aka ceto a Oyo
Daliban Oyo da sojoji suka ceto a daji. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa daya daga cikin malamai ya rasa rayuwa a hannun maharan, sai dai ranar 10 ga Yuli 2026 ne sojoji da jami'an DSS suka hada kai suka ceto sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

An kama iyalan masu garkuwa

Majiyoyin tsaro da dama sun bayyana cewa an saki bidiyon tambayoyin da aka yi wa mata da ya'ayan masu garkuwar har ya samu yaɗuwa zuwa hannun masu garkuwa da mutanen, lamarin da ya girgiza su.

“Nan take masu garkuwa suka fara nuna sassauci, suka fara tuntuɓar jami’an tsaro akai-akai maimakon biris bayan sun gabatar da buƙatunsu,”

In ji wata majiya.

A cewar majiyoyin, daga nan ne ’yan ta’addar suka gabatar da tayin sakin ɗaliban da malamai da aka sace a madadin a saki matansu tare da ba su tabbacin za su dawo wajensu.

Sai dai hukumomin tsaro sun yi watsi da tayin, suna cewa dole ne da farko a saki waɗanda aka sace, sannan masu garkuwar su miƙa wuya ko kuma su fuskanci kamu ko kashewa yayin farmakin soji.

Kara karanta wannan

Dalibai da malaman da aka sace a Oyo sun kubuta, an samu bayanai

Masu bincike sun yi imanin cewa kama iyalan ’yan ta’addar ya rage yiwuwar su cutar da waɗanda suka yi garkuwa da su, saboda tsoron abin da ka iya faruwa ga nasu iyalan.

An kuma gano cewa yayin da ake ci gaba da tattaunawa, rundunar haɗin gwiwa ta ci gaba da ƙara matsa ƙaimi wajen kewaye maboyar ’yan ta’addan.

Daliban da aka ceto a Oyo
Soja na saka daliban da aka ceto a cikn mota. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yadda aka ceto daliban Oyo

Wata majiya ta bayyana cewa an bayar da umarnin ƙarshe na kai farmaki sansanin ’yan ta’addar ne a daren Alhamis bayan samun sababbin bayanan sirri.

Majiyar ta ce farmakin ya kasance cikin sauri, tsari mai kyau da kuma ƙarfin dakarun soji mai yawa, wanda ya ba ’yan ta’addar mamaki.

Majiyoyin tsaro da dama sun ƙara da cewa a makonnin da suka gabaci farmakin na ƙarshe, sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan sau da dama domin raunana ƙarfinsu da rage musu harsasai.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa a yayin farmakin, an kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da aka kama wasu takwas daga cikinsu.

Tinubu ya zauna da jami'an tsaro

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi zama na musamman da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.

Kara karanta wannan

Kano APC: 'Ayyukan da za su jawo wa Tinubu ruwan kuri'a a 2027'

Zaman ya hada da hafsoshin tsaron Najeriya, shugabannin 'yan sanda, mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da sauransu.

Duk da cewa fadar shugaban kasa ba ta fitar da rahoto kan abubuwan da suka tattauna ba, an yi hasashen zaman na da alaka da halin da kasa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng