Tofa: Shugaban Wata Hukuma a Abuja Ya Ƙi Barin Ofis duk da Tinubu Ya Sauya Shi

Tofa: Shugaban Wata Hukuma a Abuja Ya Ƙi Barin Ofis duk da Tinubu Ya Sauya Shi

  • Ana zargin Dakorinama Alabo George ya ƙi barin kujerar shugaban hukumar BCDA duk da maye gurbinsa da Shugaba Bola Tinubu ya yi
  • Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Abdulrazak Sa'ad Namdas ne sabon shugaban hukumar daga ranar 26 ga Yuni, bayan murabus din George
  • George ya yi murabus domin neman takarar gwamnan Rivers a APC kafin daga baya ya janye, kuma ya koma ci gaba da riƙe da ofishin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - An fara fuskantar rikicin shugabanci a Hukumar Bunƙasa Yankunan Kan Iyakoki ta Najeriya (BCDA), bayan rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban hukumar, Dr. Dakorinama Alabo George, ya ki barin ofis duk da sanar da wanda zai gaje shi.

Lamarin ya biyo bayan sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, wadda ta bayyana tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Abdulrazak Sa'ad Namdas, a matsayin sabon shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

Yan sandan jihohi: Barau Jibrin ya fadi amfanin shirin ga Arewacin Najeriya

Ana zargin tsohon shugaban hukumar BCDA ya ki barin ofis duk da Tinubu ya sauya shi
Abdulrazak Sa'ad Namdas da Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar BCDA, da Dr. Dakorinama George da ake zargin ya ki barin ofis. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Yadda Tinubu ya maye gurbin George

A ranar 26 ga Yuni, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanar a shafinsa na X cewa Namdas zai maye gurbin Dakorinama Alabo George.

Sanarwar ta ce George ya yi murabus ne domin neman wani muƙamin siyasa a jiharsa ta Rivers, bayan umarnin da Shugaba Tinubu ya bai wa duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 su sauka daga mukamansu kafin ranar 31 ga Maris, 2026.

Umarnin ya dogara ne da Sashe na 88(1) na Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma jadawalin zaɓe da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta fitar.

George ya janye daga neman takarar gwamna

Rahotanni sun nuna cewa George ya shiga takarar gwamnan jihar Rivers a ƙarƙashin jam'iyyar APC, inda ya fafata da wasu 'yan takara ciki har da Siminalayi Fubara, Kingsley Chinda da Tonye Cole.

Kara karanta wannan

Rashin sani: Shaguben da sanatan Amurka ya yi ga Iran kwana 5 kafin ya mutu

Takardar tantance 'yan takarar gwamna ta APC mai ɗauke da kwanan watan 11 ga Mayu, 2026, ta nuna cewa an tantance George kuma an ba shi damar shiga zaɓen fitar da gwani.

Sai dai ya janye daga takarar a ranar zaɓen fitar da gwani domin bai wa Kingsley Chinda damar zama ɗan takarar jam'iyyar a Rivers.

Rahoto ya ce George ya ƙi barin ofis

Majiyoyi sun shaida cewa duk da yin murabus domin neman takara, George bai miƙa ragamar aiki ga wani ba, kuma ya ci gaba da amfani da kadarorin ofishin BCDA.

Bayan ya gaza samun tikitin takarar gwamna, rahotannin sun ce ya koma bakin aikinsa a hukumar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya ta kuma yi zargin cewa wasu jami'an gwamnati na mara masa baya, ciki har da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda George ya taɓa yi wa aiki a matsayin Kwamishinan Ayyuka lokacin Wike yana gwamnan Rivers.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jaridar ta ce ba ta samu damar tabbatar da cewa George ya yi murabus daga BCDA kafin sanar da maye gurbinsa ba.

Kuma babu wata sanarwa daga Dakorinama Alabo George da ke mayar da martani kan zargin cewa ya ƙi barin ofishinsa bayan Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da maye gurbinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com