Buhari: Ka rike Jam’iyyar APC domin a tuna da kai a tarihin Najeriya Inji Abu Ibrahim

Buhari: Ka rike Jam’iyyar APC domin a tuna da kai a tarihin Najeriya Inji Abu Ibrahim

Sanata Abu Ibrahim, wanda shi ne shugaban kwamitin Amintattu na kungiyar CNNi, ya ce shugaba Muhammadu Buhari zai kafa sunansa a tarihi ne idan ya rike APC.

Abu Ibrahim ya bayyana cewa sai idan har shugaban kasar ya hana jam’iyyar APC wargajewa ne sannan za a rika tunawa da shi ko bayan ya bar kan karagar mulki a Najeriya.

Ibrahim ya yi wannan bayani ne lokacin da ya jagoranci ‘Yan kungiyarsa ta Magoya bayan Buhari a fadin Najeriya (wanda aka santa da NCBSG), zuwa fadar shugaban kasar.

Jagoran kungiyar na CNNi ya fadawa shugaban kasar muhimmancin rike jam’iyyar APC daga wargajewa, domin kuwa da jam’iyyar ya samu damar iya mulkin Najeriya.

Tsohon Sanatan da ya wakilci Kudancin Katsina, ya ce Muhammadu Buhari ya yi amfani da jam’iyyar APC ne wajen cin ma burinsa na zama shugaban kasa har sau biyu.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta na barazanar hukunta Ministan Buhari a Katsina

Buhari: Ka rike Jam’iyyar APC domin a tuna da kai a tarihin Najeriya Inji Abu Ibrahim
Abu Ibrahim ya ce idan Buhari ya rike APC idan ya na so a tuna da shi bayan ya bar mulki
Asali: Facebook

‘Dan siyasar ya kuma yi magana da Buhari game da sha’anin tattalin arziki, musamman abin da ya shafi Talakawan Najeriya, da kuma hadin kan-kasar da sunan da zai bari.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Abu Ibrahim ya roki shugaban kasar ya kawo tsare-tsaren da za su sa jama’a su godewa mulkin APC, tare da kira ya sa jam’iyyar a gabansa.

A cewar Sanata Ibrahim, jama’a da-dama su na ganin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya ke rike da jam’iyyar APC. Buhari zai sauka daga mulki ne a shekarar 2023.

Shugaban tafiyar, ya fadawa shugaban kasar cewa: “Dinbin Matasan da su ka goyi bayanka da APC a zaben da wuce, sun yi tattaki, kuma su na sa ran ganin abin da ya fi haka.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel