Abubuwan da aka fahimta da mulkin Buhari daga wasikar NSA da ta fito fili

Abubuwan da aka fahimta da mulkin Buhari daga wasikar NSA da ta fito fili

A cikin ‘yan kwanakin nan ne aka bankado wasu boyayyun wasiku da NSA Babagana Monguno ya rubuta a bara. A cikin wasikun an fahimci cewa Buhari ya na fama da rikicin cikin gida.

Jaridar Premium Times da ta fito da wasikun, ta bayyana abubuwan da aka fahimta kawo yanzu:

1. Ba a ga maciji tsakanin COS da NSA

Wasikun da su ka fito daga ofishin NSA sun nuna cewa akwai sabani tsakanin Babagana Monguno da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa watau Malam Abba Kyari.

2. Hadimin Buhari ya na dawo da Shugaban kasa baya

A cikin wadannan wasiku da yanzu su ke yawo a Najeriya, an fahimci cewa a wasu lokutan Abba Kyari ya kan yi watsi da umarnin shugaban kasa, ya bada sabon umarni da kansa.

3. Abba Kyari ya na juya akalar Gwamnati

Haka zalika kawo yanzu an fahimci cewa kusancin Abba Kyari da shugaban kasa ta sa ya na rike da madafan iko a gwamnatin mai-ci. Kyari ya na cikin wadanda su ka fi kowa karfin iko.

KU KARANTA: Rigima ta barke tsakanin manyan Hadiman Shugaban Najeriya

4. Badakalar kwangilar makamai

Kyari ya yi amfani da ofishinsa ya ba wani kamfani kwangilar makaman ‘Yan Sanda bayan shugaban kasa ya yi magana da wani kamfani a UAE, wanda hakan na iya jawo abin kunya.

5. COS ya na zama da Shugabannin Sojoji da Jakadun kasashe

Wasikun da Babagana Munguno ya fitar sun bayyana cewa Abba Kyari ya kan kira taro har ya jagoranci zama da Hafsun Sojoji da Jakadun kasashen waje duk da bai da wannan hurumi.

6. Shugaban Ma’aikatan fada Hadimin Shugaban kasa ne

Janar Babagana Munguno mai ritaya, ya nuna cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ba komai ba ne face Hadimin shugaba Buhari a dokar kasa da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng