Ana shari’a tsakanin ‘Yar kasuwar da aka yi amfani da hotunanta wajen kamfe a zaben 2019 da PDP

Ana shari’a tsakanin ‘Yar kasuwar da aka yi amfani da hotunanta wajen kamfe a zaben 2019 da PDP

A Ranar Talatar nan, wata babban kotun tarayya da ke zama a Legas, ta sa ranar da za a saurari karar da wata ‘Yar kasuwa Amudat Adeleke, ta shigar a kan wasu manyan jam’iyyar PDP.

Misis Amudat Adeleke ta na kuka a kan yadda jam’iyyar PDP ta yi amfani da hotunanta a kan allon yakin neman zabe, ba tare da izninta ba. Wanda ta ke tuhuma shi ne Dr. Bukola Saraki.

Bukola Saraki shi ne Darektan yakin neman zaben Atiku Abubakar a 2019 a karkashin jam’iyyar PDP. Sauran wadanda ta ke kara sun hada da shi Atiku Abubakar, Peter Obi da jam’iyyar.

Lauyan wannan Baiwar Allah, Kingsley Iheakaram, ya bukaci kotu ta tursasawa wadanda ake tuhuma su biya ta Naira miliyan 45 sakamakon amfani da hotonta wajen yakin neman zabe.

Bayan haka wannan ‘Yar kasuwa ta bukaci ayi maza a cire hotunanta daga kan allon PDP da aka baza a wurare irinsu Onikan, Costain, Apongbon, Yaba, Ilupeju da Ikorodu a jihar Legas.

KU KARANTA: Yadda Hadimin Buhari ya ke kawo matsala wajen sha'anin tsaro

Ana shari’a tsakanin ‘Yar kasuwar da aka yi amfani da hotunanta wajen kamfe a zaben 2019 da PDP
Bukola Saraki ne Darektan jirgin yakin neman zaben Atiku a PDP
Asali: UGC

Iheakaram wanda ya ke kare wannan Mata ya kuma roki Alkali ya tabbatar da cewa amfani da hotunanta a Najeriya da wajen kasar keta alfarmarta ne, wanda hakan ya sabawa dokar kasa.

Lauyan da ke kare ‘Yan siyasar na PDP, Eyitayo Jegede ya shaidawa kotu cewa wannan mata ta dauki hoton ne da kanta tare da wasu ‘yan kasuwa, sannan ta nuna goyon bayanta ga PDP.

Babban Lauya Eyitayo Jegede ya kuma fadawa kotu cewa sauran wadanda ake tuhuma a karar ba su san wannan Baiwar Allah ba. Wannna ya sa roki kotu ta yi fatali da shari’ar gaba daya.

Bayan sauraron kowane bangare, Alkali mai shari’a Ayokunke Faji ya dakatar da cigaba da sauraron karar har sai zuwa Ranar 22 ga Watan Afrilu domin a yanke hukuncin da ya dace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel