Kotun koli: PDP za ta dawo mulki a Jihar Imo – Inji Shugaban Jam’iyya Secondus

Kotun koli: PDP za ta dawo mulki a Jihar Imo – Inji Shugaban Jam’iyya Secondus

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Mista Prince Uche Secondus, ya bayyana cewa akwai hanyoyi da-dama da za su ka dogara da su domin su karbe mulki a jihar Imo.

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta nuna cewa za ta karbe mulki daga hannun APC a Imo. PDP ta lashe zaben gwamna a jihar har ta fara mulki, kafim kotun koli ta tsige ta.

Prince Uche Secondus ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa su na sa ran kotun koli za su yi watsi da hunkuncin da su ka yi domin akwai matsala idan har aka tafi a haka.

Jam’iyyar PDP da ‘Dan takararta, Emeka Ihedioha, sun koma babban kotun kasar domin kalubalantar mikawa Sanata Hope Uzodinma na jam’iyyar APC mulki.

Uche Secondus ya yi magana da ‘Yan jarida a Ranar Talata, 18 ga Watan Fubrairun 2020, ya ce yawan kuri’un da aka kada ya fi karfin wadanda aka tantance a jihar.

PDP ta bakin shugabanta, ta ce ta bayan-fage APC ta zagaya ta samu mulki. “Uzodinma da APC sun yaudari kotun koli da cewa an yi masu watsi da kuri’a 213, 495’.

KU KARANTA: Gwamnoni 9 da kotu ta raba su da kujerunsu a Najeriya

Kotun koli: PDP za ta dawo mulki a Jihar Imo – Inji Shugaban Jam’iyya Secondus
Uce Secondus ya ce Jam’iyyar PDP za ta koma kan mulki a Imo
Asali: Twitter

“Idan har aka kyale karyar da aka yi wa kotun koli ta zauna, to zai zama yawan kuri’un da aka kada a zaben, ya haura yawan wadanda aka tantance su yi zabe.” Inji sa.

Shugaban PDP ya yi bayani filla-filla da cewa: “Yawan mutanen da aka tantance su yi zaben shi ne 823, 743, amma kuma ainihin kuri’un da aka kada su ne 731, 485.”

PDP ta ce: “Don haka idan aka kara da kuri’u 213,695 na APC da Uzodinma, zai sa yawan wadanda su ka yi zaben su fi karfin asalin wadanda aka tantance a zaben jihar.”

Mista Secondus ya kara da cewa: “Wannan ba za ta yiwu ba. Babu dalilin mu kafa mummunan tarihi.” A na sa ra’ayin ba a saba ganin irin wannan hukunci a kotu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel