Gwamnati Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa NIN ba Ta Gano Masu Garkuwa da Mutane

Gwamnati Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa NIN ba Ta Gano Masu Garkuwa da Mutane

  • Hukumar bayar da shaidar 'dan kasa ta NIMC ta y karin haske a kan dalilin da ya sa ake gaza bibiyar 'yan ta'adda da sauran masu garkuwa da mutane
  • Hukumar ta bayyana cewa NIN tsarin tantance mutum ne, ba kayan leƙen asiri ko bibiyar mutanen kasar nan da ke da lamabar shaidar ba
  • Ta jaddada tsarin da za a iya amfani da ita wajen gano masu aikata laifi ta lambar shaidar dan kasa da su suka mallaka, domin ba aikinta kada ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babbar Darakta Janar ta Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa ta Kasa (NIMC), Abisoye Coker-Odusote, ta bayyana dalilin da ya sa ba a iya gano masu garkuwa da mutane da 'yan ta'adda ta hanyar Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN).

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Yadda za a kai korafi ga EFCC kan zargin damfara, badakala

Ta bayyana haka ne duk da muhimmancin tsarin wajen inganta tsaron Najeriya, wanda kuma aka umarci kowanne dan kasa ya tabbata ya mallaka.

NIMC ta ce ba ta bibiyar jama'a ta NIN
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

Da take magana a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television, Coker-Odusote ta ce sau da yawa masu garkuwa da mutane kan yi amfani da wayoyin mutanen da suka sace maimakon layukansu da aka yi wa rajista.

Dalilin da NIN ba ya kama yan ta'adda

Jaridar Punch ta wallafa cewa Abisoye Coker-Odusote ta kara da cewa akwai wata fahimta da ke cewa wasu daga cikin masu garkuwa da mutane na iya kasancewa ba 'yan Najeriya ba ne, kuma ana iya shigo da su ƙasar awanni 48 zuwa 72 kafin su aikata laifin.

A cewarta:

"Akwai wata fahimta cewa watakila waɗannan masu garkuwa da mutane ba 'yan Najeriya ba ne, ana shigo da su ƙasar ne sa'o'i 48 ko 72 kafin a aikata satar mutane. Ba ina tabbatar da haka ba ne, amma idan hakan ne, to ba za su kasance cikin bayananmu ba. Waɗannan na daga cikin yiwuwar da muke gani."

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Ta jaddada cewa duk da muhimmancin NIN a tsarin tantance mutane da tsaron ƙasa, masu laifi kan yi amfani da dabaru da ke sa a yi wahalar gano su, ciki har da amfani da wayoyi na waɗanda suka sace.

Ba a leken asiri da NIN

Hukumar ta jaddada cewa NIN lamba ce ta musamman mai lambobi 11 da NIMC ke bai wa 'yan Najeriya da kuma baƙin da ke zaune a ƙasar bisa doka, kamar yadda Dokar NIMC ta shekarar 2007 ta tanada.

NIMC ta ce ba aikinta ne kawai zai gano yan ta'adda ba
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, katin shaidar dan NIN Hoto: @officialABAT/@nimc_ng
Source: Twitter

Gwamnatin Tarayya ta mayar da NIN wani muhimmin ɓangare na tsarin tsaro ta hanyar wajabta haɗa layukan waya da NIN domin ƙarfafa tantance mutane, sauƙaƙa bincike da kuma yaƙi da laifuffuka.

Sai dai NIMC ta nanata cewa NIN tsarin kula da bayanan shaidar mutum ne kawai, ba tsarin bibiyar mutane ko leƙen asiri ba, kuma gano masu laifi na buƙatar haɗin gwiwar hukumomin tsaro, kamfanonin sadarwa da sauran hukumomin da abin ya shafa.

An zauna kan yaki da yan ta'adda

A baya, mun wallafa cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi babban taron tsaro da shugabannin rundunar soji da hukumomin leken asiri a fadar shugaban kasa saboda karuwar matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Taron ya zo ne bayan dakarun Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda kusan 300 a jihohin Zamfara da Katsina tare da kashe wani babban kwamandan 'yan bindiga yayin da ake kokarin kakkabe rashin tsaro a kasar nan.

Haka kuma ya zo bayan an kai wa sansanin soja na Mairari hari a Arewa maso Gabas, kuma an kai fiye da hare-hare 13 kan sansanonin soja a 2026 kadai da karin wasu hare-hare a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng