Akande: Masoyan Adams Oshiomhole za su maka Shugaban PGF a gaban Alkali

Akande: Masoyan Adams Oshiomhole za su maka Shugaban PGF a gaban Alkali

Magoya bayan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, sun yi barazanar kai karar Darekta Janar na kungiyar gwamnonin APC, Salihu Lukman, a gaban kotu.

Wata kungiya ta Masoyan Kwamred Adams Oshiomhole a karkashin jam’iyyar APC a jihar Edo, su ka bayyana wannan matsaya da su ka cin ma ta bakin shugabanninsu a jiya.

Kungiyar ta yi wannan bayani ne a jawabin da ta fitar da bakin Francis Inegbeneki da Suleiman Bagudu, ta na zargin Salihu Lukman da cewa ‘Dan jam’iyyar PDP ne a boye.

Salihu Lukman ya rubutawa kwamitin Cif Bisi Akande da aka kafa domin yin sulhu a jam’iyyar APC wasika, inda ya soki salon tafiyar APC a karkashin jagorancin Oshiomhole.

Wannan kungiya ta Magoya bayan shugaban jam’iyyar na kasa ta ce wasikar da Lukman ya rubuta da inuwar gwamnonin APC, kokarin ci wa Adams Oshiomhole mutunci ne.

KU KARANTA: An kafa 'Yan kwamitin da za su yi aikin sulhu a Jam'iyyar APC

Akande: Masoyan Adams Oshiomhole za su maka Shugaban PGF a gaban Alkali
Wasu su na zargin Adams Oshiomhole da kawowa APC matsala
Asali: Twitter

Francis Inegbeneki da Suleiman Bagudu sun fadawa Lukman ya janye maganganun da ya yi. Idan har bai yi hakanba bayan mako guda, za su hadu da shi a gaban Alkali a kotu.

“Mun ba wannan ‘Darektan kungiya’ kwanaki bakwai ya fito ya janye kalamansa masu suka, ya kuma ba Kwamred Adams Oshiomhole hakuri ko ya fuskanci shari’a a kotu.”

“Yayin da babu komai a cikin wannan takarda sai zallan shirme, daga ranar da ya rubuta wannan wasika, ya tashi daga shugaban kungiyar gwamonin APC.” Inji 'Yan kungiyar.

A cewar Lukman, tun da Oshiomhole ya karbi ragamar jam'iyyar, APC ta tashi daga jam'iyyar siyasa domin babu wani kwamiti na jam'iyyar da ke aiki yadda ya kamata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel