Kamfanin Dangote Ya Sa Ladar N500000 ga Wadanda Suka Tona Asirin Direbobinsa

Kamfanin Dangote Ya Sa Ladar N500000 ga Wadanda Suka Tona Asirin Direbobinsa

  • Dangote ya ƙaddamar da shiri na musamman don yaƙi da amfani da manyan motocin safararsa ta hanyoyin da suka sabawa doka
  • Kamfanin ya yi alƙawarin ba da kyautar kuɗi har ₦500,000 ga duk wani mutum da ya bayar da sahihin bayani da zai taimaka masa
  • Akwai direbobi da ke amfani da motocin kamfanin Dangote wajen jigilar kaya ko mutane domin su karbi kudi ba bisa ƙa'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Kamfanin Dangote ya kawo wani shiri na fasa kwai da nufin kawo karshen amfanin motocinsa ba bisa ka’idar aiki ba.

Akwai direbobin da suke amfani da manyan motocin Dangote wajen daukar mutane ko kaya ta hanyoyin da ba a yarda da su ba.

Dangote
Aliko Dangote da motocin kamfaninsa Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Dangote zai biya N500, 000 a sa wa direbobi ido

Duk wanda ya tona asirin masu yin wannan danyen aiki zai tashi da kudi har N500, 000 kamar yadda The Cable ta ruwaito a dazu.

Kara karanta wannan

China: Macizai masu haɗari sun fara kisa da ambaliya ta yi kaca kaca da gonakinsu

Idan mutum ya bada bayani na kwarai wanda zai jawo a yi nasarar jigilar haramtattun kaya ka mutane a motocin zai samu ladar,

Kamfanin ya sanar da haka ne ta bakin wata sanarwa daga aka samu daga DIL ranar Lahadi.

DIL ya yi gargadi cewa babu abin da ya halatta a motar illa wanda kamfanin ko takwarorinsa suka amince da shi a Najeriya.

Kayan da aka amince motocin Dangote su dauka

Motar kamfanin simintin Dangote tana da izinin daukar siminti da sinadaran limestone, gypsum, coal da kuma clinker ne kawai.

Sanarwar ta ce su kuma motocin sukarin kamfanin Dangote ba za su dauki komai ba illa shi sukarin.

The Guardian ta rahoto cewa motocin kamfanin NASCON an tanade su ne da nufin jigilar gishirin Dangote da sauran kayan DanQ.

Akwai motocin da aka ware su dauki jakunkuna da kayayyakin daukar kayan Dangote.

A gefe guda, an yi wa motocin matatar Dangote izinin daukar kayan polypropylene sai motocin kamfanin taki su dauki buhunan takin zamani.

Dangote
Wasu motocin kamfanin Dangote a hanya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wadanne bayanai Dangote yake bukata?

Kara karanta wannan

Bayan saukar Pantami a filin jirgi, gwamnatin Gombe ta yi barazanar bincike

Masu tonon sililin za su aika wa kamfanin da bayanin nau’in mota, lambar mota, launin mota, wuri, da bayanin kayan da ake tafe da su.

Bugu da kari ana son daukar hoto idan har za a iya domin taimaka wa kamfanin na Dangote wajen gudanar da binckike na musamman.

"Duk mutumin da aka samu da tabbataccen bayanin da ya kai ga cafke wadanda suke jigilar haramun ko ga karbo haramtattun kaya da ake jigila a motocin Dangota za su samu ladar N500, 000."

- DIL

Dangote ya hada-kai da jami’an tsaro irinsu ‘yan sanda wadanda za su cafke direbobin da ake zargi da neman kudi da motocinsa.

DIL ya ce makasudin yin hakan shi ne kare dukiyoyinsa, yin kasuwanci mai tsabta da kuma ganin an yi maganin masu saba wa doka.

Dangote zai rika raba mai a kyauta

A baya matatar man Dangote ta kaddamar da shirin rarraba man fetur kai tsaye ga dillalai ta hanyar amfani da manyan motoci guda 1,000.

Motocin masu amfani da iskar gas (CNG) ne domin kashe kudin da ake yi a baya. Wannan mataki zai kawo raguwar farashin fetur a fadin Najeriya.

A jihohin Kudu Maso Yamma da Legas, an sayar da lita a kan N8411 yayin da a Abuja da wasu jihohi kudin lita ya koma N851 wancan lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng