Babu wata bukatar a taba tsarin Majaliar Tarayya – Ahmed Yariman-Bakura

Babu wata bukatar a taba tsarin Majaliar Tarayya – Ahmed Yariman-Bakura

Ahmed Sani Yariman-Bakura wanda ya rike kujerar Sanata tun daga 2007 zuwa 2019, ya nuna cewa kudin da ‘Yan majalisa su ke tashi da shi duk wata Najeriya bai yi yawa ba.

Sanata Ahmad Yariman-Bakura ya ce albashin Sanatoci bai wuce abin da gwamnonin jihohi su ke samu ba, ya ce ‘Yan majalisar wakilai ba ma su samun abin da ya kai hakan.

Tsohon gwamna Yariman-Bakura ya kare ‘Yan majalisar tarayyar inda ya ce babu bukatar a rage yawansu, idan har aka yi la’akari da yawan al’ummar da ake da ita a Najeriya.

Sanata Yarima ya kuma nuna cewa bai ga laifi don tsofaffin gwamnoni sun cika Majalisar dattawa ba, a cewarsa ko a Amurka da Ingila, Dattawa ne su ke zama Sanatoci.

Duk da aikin ‘yan majalisa bai kai na sauran bagare nauyi a Najeriya ba, tsohon Sanatan ya nuna cewa babu bukatar ace za a maida aikin majalisa ya zama na lokaci bayan lokaci.

KU KARANTA: Malamai sun ga cewa zan zama Shugaban kasa - Yarima

Babu wata bukatar a taba tsarin Majaliar Tarayya – Ahmed Yariman-Bakura
Yariman-Bakura ya ce 'Yan Majalisar Tarayya sun cancanci albashinsu
Asali: Twitter

Yariman-Bakura wanda ya yi Sanata sau uku a jere a Zamfara ya ce ‘Yan majalisa su na bukatar kudi domin su yi aikin da ke gabansu. Ya ce: “Don haka kudinsu bai yi yawa ba.

“Idan babu kudin aiki, ta ya ‘Dan majalisa zai rika zagayawa; akwai bukatar ka tafi sa-ido, za ka ziyarci mutanen Mazabar ka. Idan babu kudi ya za ka yi wannan?” Ya tambaya.

Jigon na APC ya hakura da kujerar majalisa ne a zaben 2019, a karshe jam’iyyarsa ta APC ba ta iya kafa gwamnati ba duk da ta lashe zabe a sakamakon wani rikicin cikin gida.

Babban ‘Dan siyasar ya yi wannan jawabi ne a lokacin da Jaridar Daily Trust ta yi hira da shi. Yarima wanda yanzu ya koma makaranta, ya na burin fitowa takara a zaben 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://twitter.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel