Gwamnatin Tarayya Ta Canza Shawara kan Kara Kudin WAEC da NECO a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin karin kudin rajistar jarabawar kammala sakandire ta WAEC da NECO a shekarar 2027
- Ma'aikatar Ilimi ta ce za a sake nazarin shirin karin kudin jarabawar bayan tuntubar masu ruwa da tsaki
- Tun farko dai gwamnatin ta ce karin kudin ya samo asali ne daga tsadar gudanar da harkokin jarabawa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ƙara kudin rajistar jarabawa biyu na kammala makarantun sakandire watau WAEC da NECO a shekarar 2027.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne domin bai wa masu ruwa da tsaki damar fadar ra'ayoyinsu kafin yanke hukuncin karshe.

Source: Facebook
Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook kuma Legit Hausa ta gani yau Litinin, 13 ga watan Yulin 2026.
Ta tabbatar da cewa ta janye wasikar da ta fitar ranar 18 ga Yunin 2026 wadda ta kunshi shirin karin kudin rajistar jarabawar, domin a sake yin cikakken nazari kan batun.
Dalilin dakatar da shirin a 2027
Ma'aikatar ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne bayan korafe-korafe da ra'ayoyin da jama'a suka bayyana kan shirin karin kudin.
A cewarta, an yi tunanin sake duba kudin rajistar ne saboda tsadar gudanar da jarabawar da ta karu, duk da cewa kudin rajistar ya dade ba tare da wani sauyi ba.
Ma'aikatar ta ce daga cikin abubuwan da suka kara tsada akwai jigilar kayan jarabawa, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha, tabbatar da inganci da sauran muhimman ayyukan gudanar da jarabawa.
Minista ya ba da umarnin dakatarwa
Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ba da umarnin dakatar da shirin domin gwamnatin tarayya ta ci gaba da aiwatar da manufofi bisa tuntuba, gaskiya da kuma hujjoji.
Ma'aikatar ta ce wannan mataki ya nuna kudirin gwamnati na tabbatar da cewa duk wata manufa da za ta shafi miliyoyin dalibai da iyalansu an yi mata cikakken nazari tare da la'akari da muradun kasa.

Source: Facebook
Za a tuntubi masu ruwa da tsaki
Ta bayyana cewa za a gudanar da tattaunawa da hukumomin shirya jarabawa, ma'aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu, shugabannin makarantu, kungiyoyin iyaye, kungiyar kwadago da sauran masu ruwa da tsaki kafin a dauki kowace matsaya.
Ma'aikatar ta jaddada cewa ba za a aiwatar da duk wani karin kudin rajistar jarabawa ba har sai an kammala wannan shawarwari.
A karshe, ma'aikatar ta gode wa 'yan Najeriya kan fahimta da goyon bayan da suke bayarwa, tare da alkawarin ci gaba da sanar da jama'a duk wani ci gaba da aka samu.
An ƙayyade shekarun zana WAEC da NECO?
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan batun mafi karancin shekarun zana jarabawar fita sakandire WAEC, NECO da NABTEB.
Gwamnatin ta bayyana cewa babu inda ta ƙayyade cewa dole zai dalibai ya kai zhekara 18 kafin a ba shi damar zama jarabawar WAEC da NECO.
Karamin ministan ilimi, Dr Tanko Sununu ya ce jarabawar share fagen shiga jami'o'i ce aka sanya wa dokar cika shekara 18
Asali: Legit.ng

