Ministan Tinubu da ake Zargi da Amfani da Takardun Bogi Ya Yi Magana a Kotu
- Babbar Kotun Tarayya ta fara sauraron shari'ar tsohon Ministan Bola Tinubu kan zarge-zarge shida da suka shafi amfani da takardun karatu na bogi
- Gwamnatin Najeriya na zarginsa Uche Nnaji da gabatar da takardun digiri da na NYSC na bogi da kuma karɓar albashi ta hanyar yaudara
- Ana tsaka da wannan dambar ne sai Uche Nnaji ya yi murabus daga kujerarsa ta ministan kirire-kirkire da fasaha gabanin a kai shi kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ministan Kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya musanta tuhume-tuhume shida da ake yi masa da suka haɗa da amfani da takardun bogi.
Wannan na zuwa ne bayan an gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda aka fara zama a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2026.

Source: Twitter
Channels TV ta wallafa cewa hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai suna ICPC ce ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari'a Joyce Abdulmalik.
Zargin da ake yi wa Nnaji
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ana zargin Nnaji da gabatar da takardar shaidar digiri ta bogi daga Jami'ar UNN da kuma takardar kammala hidimar ƙasa ta NYSC lokacin tantance shi domin zama minista a shekarar 2023.
Haka kuma, ana tuhumarsa da karɓar kusan Naira miliyan 29.5 a matsayin albashi da wasu alawus ta hanyar yaudara, tare da zargin safarar kuɗi.
Bayan ya musanta zargin, lauyansa mai mukamin SAN, Ogwu Onoja, ya sanar da kotu cewa ya shigar da buƙatar a ba wanda yake karewa beli.
kotu ta ba da belin Nnaji
Lauyan masu gabatar da ƙara ya bayyana cewa a shirye su ke su fara shari'ar kuma suna da shaidu uku. Ya kuma ce ba ya adawa da neman belin, yana mai cewa hukuncin yana hannun kotu.
Mai Shari'a Abdulmalik ta amince da ba Nnaji beli kan Naira miliyan 20 tare da mutum ɗaya da zai tsaya masa da irin wannan kuɗi.
Kotun ta gindaya cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance ma'aikacin gwamnatin tarayya mai mataki na15 ko sama da haka, kuma ya mazauni a gari da ya shafe shekaru hudu a wuri daya.

Source: Twitter
Har ila yau, dole ne ya gabatar da takardar aikinsa da kuma bayanan albashinsa na watanni uku da suka gabata domin tantancewa.
Kotun ta kuma umarci Nnaji ya miƙa fasfo ɗinsa na ƙasa da sauran takardun tafiya, kafin ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga Satumba, 2026, domin fara sauraron shaidu.
Nnaji ya daukaka kara
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya ɗaukaka ƙara kan umarnin kotu da ya ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa na ICPC damar kama shi.
Kotu ta bayar da umarnin ne saboda ana zargin tsohon minista a gwamnatin Bola Tinubu da takardun jabu da kuma amfani da hanyar yaudara wajen fara karban albashi daga gwamnatin Najeriya.
Hukumar ICPC ta ce Nnaji ya yi watsi da gayyata da dama da aka aika masa dangane da binciken zargin jabun takardar digiri da ta NYSC wanda ya sa a samo umarnin kotu, amma Nnaji ya daukaka kara a ranar ranar 18 ga Yuni 2026.
Asali: Legit.ng

