Buhari ya sha caccaka a kan goyon bayan makudan kudaden da ake biyan yan majalisa

Buhari ya sha caccaka a kan goyon bayan makudan kudaden da ake biyan yan majalisa

Kungiyar kwadago da kungiyar lauyoyin Najeriya sun nuna rashin amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa da ya yi kudin da ake biyan yan majalisa bai fi karfin aikin da suke yi ba.

Sun bayyana cewa bai dace a ce Shugaban kasar ya yi watsi da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma wahalar da yan Najeriya ke sha ba yayin goyon bayan makudan kudaden da ake biyan yan majalisar ba.

Shugaban kungiyar tattaunawa na ma’aikatan gwamnati na kasa (bangaren kungiyar kwadago), AbdulRauf Adeniji, a wata hira da jaridar The Punch a Abuja a ranar Lahadi, ya ce bangaren kwadago ne ke samar da arzikin kasa ba wai yan majalisa ba.

Buhari ya sha caccaka a kan goyon bayan makudan kudaden da ake biyan yan majalisa
Buhari ya sha caccaka a kan goyon bayan makudan kudaden da ake biyan yan majalisa
Asali: Twitter

Babban sakataren kungiyar lauyoyin Najeriya, Mista Kunle Edun, a wani hira da manema labarai, ya ce yan majalisa na karban makudan kudade da bai dace da halin da tattalin arziki ke ciki ba yayin da mafi karancin albashin kasar ke a kan N30,000 duk wata.

KU KARANTA KUMA: Na ji Obaseki na fadin a kashe Oshiomhole – Okosun

Idan za ku tuna a makon da ya gabata ne a yayin kaddamar da mujjalar majalisar wakilai ne shugaba Buhari ya ce bai dace ba a ce yan Najeriya su dunga yi wa yan majalisa kallo a matsayin wadanda albashin su ya fi karfin aikin da suke yi.

Sai dai Adeniji ya ce bai dace ba Shugaban kasar ya yi watsi da wahalar da yan Najeriya ke sha ba sannan ya yi kokarin goyon bayan tarin kudaden da yan majalisa ke karba a matsayin albashi da alawus kan dan aikin da suke yi sannan babu abun da suke karawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar.

A wani labarin kuma mun ji cewa Ahmed Sani Yariman-Bakura wanda ya rike kujerar Sanata tun daga 2007 zuwa 2019, ya nuna cewa kudin da ‘Yan majalisa su ke tashi da shi duk wata Najeriya bai yi yawa ba.

Sanata Ahmad Yariman-Bakura ya ce albashin Sanatoci bai wuce abin da gwamnonin jihohi su ke samu ba, ya ce ‘Yan majalisar wakilai ba ma su samun abin da ya kai hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel