An Yi Rashi: Mutuwa Ta Dauke Mahaifiyar Dan Takarar Gwamnan ADC

An Yi Rashi: Mutuwa Ta Dauke Mahaifiyar Dan Takarar Gwamnan ADC

  • Dan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a jihar Legas, Gbadebo Rhodes-Vivour, ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Nkechi Stella Rhodes-Vivour
  • Iyalan marigayiyar sun bayyana ta a matsayin mace mai cike da kauna kuma uwa ta gari wadda za a yi kewarta sosai
  • A cikin sanarwar da aka fitar kan rasuwarta, an ce za a sanar da ranar da za a yi jana'izar ta nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Dan takarar gwamnan jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Legas, Gbadebo Rhodes-Vivour, ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Nkechi Stella Rhodes-Vivour.

Gbadebo Rhodes-Vivour ya rasa mahafiyarsa ne yayin da yake ci gaba da shirye-shiryen fafatawa a zaben gwamnan jihar Legas na shekarar 2027 a karkashin inuwar jam'iyyar ADC.

Mahaifiyar Gbadebo ta rasu
Gbadebo Rhodes-Vivour da marigayiyar mahaifiyarsa Hoto: @GRVlagos
Source: Twitter

Rhodes-Vivour ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke 'yar kasar waje mai safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda

Rhodes-Vivour ya rasa mahaifiya

Sanarwar, wacce Olawale Rhodes-Vivour ya fitar a madadin iyalan, ta bayyana marigayiyar a matsayin mata mai biyayya, uwa mai sadaukarwa da kuma kaka abin alfahari.

"Cikin bakin ciki da kuma godiya ga Allah saboda rayuwa mai albarka da ta yi, muna sanar da rasuwar Nkechi Stella Rhodes-Vivour (née Waboso). Ta kasance mata mai biyayya, uwa mai sadaukarwa da kuma kaka. Ta kasance abar koyi wajen nuna kauna."

- Olawale Rhodes-Vivour

Iyalan sun ce za su yi matukar kewarta tare da yi mata addu'ar Allah Ya ji kanta.

"Za mu yi matukar kewarta. Allah Ya sa ruhinta ya huta cikin cikakkiyar salama."

- Olawale Rhodes-Vivour

Har ila yau, iyalan sun bayyana cewa za su sanar da cikakken tsarin jana'izar marigayiyar a wani lokaci na gaba.

An kwararo yabo ga marigayiyar

A cikin takardar sanarwar rasuwar da iyalan suka fitar, sun yi ta'aziyyar marigayiyar tare da bayyana ta a matsayin mace wacce ƙauna, tausayi da kyawawan halayenta suka yi tasiri ga rayuwar duk waɗanda suka san ta.

Kara karanta wannan

Rahoton WFP: ADC ta zargi Tinubu da jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a jihohin Arewa 9

Sun bayyana ta da cewa:

"Mata abar ƙauna, uwa mai sadaukarwa, kuma mace mai tawali'u."
"Ta kasance mai tsananin ƙauna da kyauta ba tare da gajiyawa ba. A hannayenta muka samu wurin zama, a cikin murmushinta kuma muka samu kwanciyar hankali. Ta kasance mata mai ƙauna ga mijinta, uwa mai kulawa ga 'ya'yanta. Ƙaunarta ita ce mafakarmu, kuma har yanzu tana nan daram a cikin zukatan duk waɗanda ta raya tare da su."
"Ko da yake ba ta tare da mu a zahiri, za ta ci gaba da rayuwa a cikin zukatanmu har abada."

Rhodes-Vivour zai yi takara a ADC

Gbadebo Rhodes-Vivour ya tsaya takarar gwamnan jihar Legas a zaben 2023 karkashin jam'iyyar Labour Party.

Daga bisani ya koma jam'iyyar ADC, inda ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar a zaben shekarar 2027 bayan ya lashe tikitin takara a watan Mayun 2026.

Mahaifiyar Rhodes-Vivour ta rasu
Rhodes-Vivour tare da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Hoto: @GRVlagos
Source: Twitter

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin kwamishinan ’yan sanda a jihar Legas, DCP Khan Salihu, ya yi bankwana da duniya.

An bayyana marigayin a matsayin jami’i mai kwazo, ladabi da cikakken kwarewa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa kasa hidima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng