Nan gaba kadan Gwamna Matawalle zai dawo Jam’iyyar APC – Inji Yarima

Nan gaba kadan Gwamna Matawalle zai dawo Jam’iyyar APC – Inji Yarima

Sanata Ahmed Sani Yariman-Bakura ya yi wata doguwar hira da Jaridar Daily Trust inda ya tattauna game da siyasar Zamfara da kuma shirin da ya ke yi na fitowa takara a 2023.

A wannan hira da aka fito da ita a yau Ranar 23 ga Watan Fubrairun 2020, Ahmed Sani Yariman-Bakura, ya bayyana cewa akwai yiwuwar gwamnan jihar Zamfara, ya sauya-sheka.

Tsohon gwamnan na Zamfara ya nuna cewa bai yi da-na-sanin abin da ya faru da APC a jihar ta sa a zaben 2019 ba, domin a cewarsa, gwamna mai-ci a yanzu, tsohon Yaronsa ne.

Ya ce: “Gwamnan yanzu Kwamishinana ne, ya na tare da ni a APC ya yi takarar shugaban karamar hukumar ya sha kasa, sai na ba shi Kwamishinan kananan hukumomi.”

Da aka tambayesa game da shirin da ake yi na ganin gwamna jihar Zamfaran ya koma APC, sai ya ce ka da ayi mamaki idan gwamna Bello Matawalle ya sauya-sheka ya bar PDP.

KU KARANTA: APC ta yi watsi da zargin da Matawalle ya ke yi wa Yari

Nan gaba kadan Gwamna Matawalle zai dawo Jam’iyyar APC – Inji Yarima
Yarima ya ya ce tsohon Yaronsa Matawalle zai iya barin PDP
Asali: UGC

“Mu na kokarin ganin haka, kuma mu na magana a kai. Kowane ‘Dan siyasa ya na son ya samu karin mutane a jam’iyyarsa, musamman gwamnoni. Hakan zai yi mani kyau.”

“Ina iya cewa mun yi nisa sosai a maganar. Kwarai kwanan nan zai sauya-sheka." Inji Yariman Bakura, wanda wasu Magoya bayansa a yanzu su ke komawa PDP a jihar Zamfara.

Sanata Yariman-Bakura ya ce jama’a ba su fahimci siyasa ba, a na sa hangen, gwamna Matawalle ya na sharan-fage ne domin sai ya gane na-kusa da shi, sannan zai koma APC.

Ahmed Yariman-Bakura ya ke cewa kafin zabe ne ya ke goyon bayan wani ‘Dan takara, amma a cewarsa daga kafa gwamnati, ya na tare da kowa ba tare da la'akari da jam’iyya ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel