Siyasar Najeriya
Legit.ng ta kawo muku jerin wasu mutane 7 wadanda shakikan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, kuma amintattu a wajensa, wadanda suka dade tare dashi, karanci tun daga shekarar 2003, yayin da wasu kuma tun suna kanana.
Gwamnan jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya rattafa hannu kan kudurin haramta biyan tsofaffin gwamnonin jahar kudaden fansho inda suka lakume miliyoyi, da wannan sa hannu na gwamna kudurin ta zama dika.
Jiya ne Jam’iyyar PDP ta rabe gida 2, wasu ‘Yan taware sun bude R-PDP a Adamawa. Babban ‘dan siyasar nan Umar Ardo, ya ce ya jagoranci wannan tafiya ta taware ne saboda rashin bin ka’ida.
Mukhtar Koguna ya fadi yadda ya ji da kotu ta hana sa kujerar Gwamna ana shirin hawa mulki ana saura kwana 5 a rantsar da shi Gwamna don haka dole ya dangana ga Allah.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da sha’awar zarcewa a kan karagar mulkin Najeriya a matsayin shugaban kasa da sunan neman wa’adin mulki na uku.
Ahmad Lawan ya bayyana sirrin hadin-kan ‘Yan Majalisar PDP da APC a karkashinsa. Lawan ya ce Sanatocin APC, PDP da YPP sun hada-kai a kan yi wa kasa hidima.
Tsohon Gwamna Fayose ya fadi abin da ya faru a zabukan da aka yi, ya na mai ya jefawa Jami’an tsaro da INEC mummunan zargi a zaben Gwamnoni Kogi da Bayelsa.
Mun kawo maku takaitaccen labarin tarihi da rayuwar David Lyon na jihar Bayelsa. Wanda shi ne ya karya lagon PDP na tsawon shekaru 20 a jihar Bayelsa.
Yayan majalisar dokokin jahar Gombe sun yi awon gaba da mataimakin kaakakin majalisar, Shuaibu Haruna dake wakiltar mazabar Kwami ta gabas ta jahar biyo bayan kada kuri’un rashin gamsuwa da shi da suka yi.
Siyasar Najeriya
Samu kari