Gwamna Abba Ya Kafa Kwamitin da Zai Tsara Masa Manufofin Tazarce a Mulkin Kano

Gwamna Abba Ya Kafa Kwamitin da Zai Tsara Masa Manufofin Tazarce a Mulkin Kano

  • Gwamnan Jihar Kano, ya kaddamar da wani kwamiti mai mutum 16 domin tsara sabon shiri na yakin neman zabensa
  • Kwamitin da ke karkashin jagorancin Dr. Aminu Magashi Garba, zai duba aiwatar da alkawuran da aka dauka a 2023
  • Alhaji Abba Kabir Yusuf ya Asma'u Jibrin, Dr. Bashir Muzakkar, da Hon. Sunusi Bature Dawakin Tofa a cikin kwamitin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin da zai tsara masa manufofin yakin neman zaben da zai shiga a farkon badi.

Kwamitin nami mutum 14 zai duba yadda aka aiwatar da manufofin da Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gabatar wa jama’a a zaben 2023.

Abba kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf da shugaban APC a wani taro Hoto: Kano a construction site
Source: Facebook

Sanar da kwamitin tsara manufofin 2027

Darektan yada labaran gidan gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa a Facebook mai dauke da bayanin.

Kara karanta wannan

Takarar Abba ta kara samun karfi kwanaki da samun goyon bayan Izala da Darika

Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce wannan kwamiti zai yi aikin da zai jagoranci inda gwamnatin Abba za ta sa gaba bayan zabe.

An sanar cewa kwamitin kwararrun zai yi aiki a karkashin jagorancin Dr. Aminu Magashi Garba da Dr. Yusuf Ya’u Gambo a matsayin sakatare.

Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo za su rika lura da duk aikin da kwamitin yake yi.

Baya ga kwararren likitan da zai jagoranci aikin, akwai shi kan shi Mai bada shawara kan harkar kiwon lafiya kuma likitan gwamna.

Mata 3 sun shiga cikin kwamitin

Kwamitin yana kunshe da shi kan shi kakakin gwamna wato Sanusi Dawakin Tofa da mata uku da za su tsara ayyuan da za ayi wa jama'a.

Cikin sunayen akwai mata irinsu Nana Asmau Jibrin da Halima Umar Sani, malamar harshen Hausa daga jami’ar Bayero ta Kano.

Wata mace a cikinsu ita ce mai taimaka wa gwamna kan ilmin mata, Injiniya Yasmin Mukhtar.

A bangaren matasa kuma akwai Muhammad Nazir Halliru, shugaban Kan-Invest da shugaban KASITDA, Dr. Bashir Abdu Muzakkar.

Kara karanta wannan

Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027

Akwai kwararru kamar Dr. Kabiru Shehu, Barr. Musa Lawan Abdullahi, Dr. Nasiru Alasan Kabo da Dr. Kabiru Ibrahim Getso.

Wannan kwamiti ya kunshi shugabannin hukumomin KNARDA da KASCO da shugaban karamar hukumar Ajingi mai-ci.

Wani hadimin gwamnan Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya fitar da sanarwar a shafinsa na Facebook.

Cikakken jerin ‘yan kwamitin tsara manufofin tazarce

1. Dr. Aminu Magashi Garba

2. Dr. Ibrahim Musa

3. Mallam Haladu Muhammad

4. Hon. Sunusi Bature Dawakin Tofa

5. Muhammad Nazir Halliru

6. Nana Asma’u Jibrin

7. Dr. Bashir Abdu Muzakkar

8. Dr. Farouk Kurawa

9. Kabiru Sani Yakubu

10. Dr. Yusuf Ya’u Gambo

11. Dr. Abdulhadi Zubairu Chula

12. Engr. Yesmin Mukhtar

13. Dr. Halima Umar Sani

14. Dr. Kabiru Shehu.

15. Barr. Musa Lawan Abdullahi.

16. Dr. Nasiru Alasan Kabo.

17. Dr. Kabiru Ibrahim Getso.

Tsofaffin ciyamomi da kansiloli sun ce sai Abba

Wata ƙungiyar tsofaffin Shugabannin Ƙananan Hukumomi da Kansiloli waɗanda suka yi aiki a shekarun 1997/1998 sun bi bayan Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Yadda alkalin CCT ya casa Tinubu, Saraki da sauran manya kafin ya kare a kurkuku

An ji labari cewa sun zo ofishinsa domin nuna goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kuma su na rokon a biya su hakkoinsu kamar yadda aka yi wa wasu.

Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Waiya wanda shi suka ziyarta dama, ya ba su N3m ya kuma yi alkawarin zai kai sauran roƙe-roƙensu ga gwmna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng