Mun yi wa tufkar hanci, babu hukumar da za ta kara satar kudin gwamnati - Majalisa
Majalisar wakilai ta lashi takobin dakatar da ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya (FG) daga karkatar da kudaden haraji da ya kamata su zuba a asusun gwamnati.
Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ne ya fadi hakan yayin taron jin ra'ayin jama'a da majalisar wakilai ta gudanar a Abuja ranar Alhamis.
"Akwai bukatar mu gaggauta daukan matakai da za su bawa gwamnati damar tsamo miliyoyin jama'a daga cikin kangin fatara da talauci.
"Alhaki ya rataya a wuyanmu na tabbatar da cewa an samar da manyan aiyuka da za su jawo hankalin ma su zuba hannun jari.
"Mun fahimci cewa ba zai yi wu a aiwatar da duk wadannan aiyuka da kudin rance daga kasashen waje ba. A saboda haka, akwai bukatar mu gimtse yawan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati.
"Sannan ya zama lallai mu inganta hanyoyin shigowa da tattara kudin haraji a cikin gida domin samun kudaden da za a yi amfani dasu wajen inganta rayuwar 'yan kasa.
"Wadannan hukumomi da ke tattara kudaden haraji su na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen taimakawa gwamnati ta cimma muradunta.
"Mu na da rahotanni a kan yadda irin wadannan hukumomi ke kashe kudaden da ya kamata su zuba asusun gwamnati, su na kashe kudaden ta hanyoyin da su ka saba da yarjejeniyar da aka kulla dasu da gwamnati.
DUBA WANNAN: NCDMB: Buhari ya bude katafaren ginin bene mai hawa 17 a Bayelsa (Hotuna)
"Rashin saka kudaden a aljihun gwamnati ne ya tilasta ranto kudade daga ketare domin gudanar da manyan aiyukan da gwamnati ta bawa fififiko.
"Ba za mu lamunci hakan ba, ba za mu bari a cigaba da tafiya a haka ba," a cewarsa.
Sannan ya cigaba da cewa; "alhakin majalisa ne ta saka ido a kan lalitar gwamnati da yadda ake kashe kudin jama'ar da mu ke wakilta.
"Alhakinmu ne mu tabbatar an yi amfani da kudi ta hanyar da ta dace, babu abinda zai hana majalisar wakilai yin amfani da karfin ikon da kundin mulki ya bata domin ganin ba a zalunci jama'a ko an ha'incesu ba ta kowacce hanya," a cewar Gbabiamila.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng