IBB @ 79: Wasu zababbun hotunan Janar Ibrahim Badamasi Babangida

IBB @ 79: Wasu zababbun hotunan Janar Ibrahim Badamasi Babangida

A yau Litinin, 17 ga watan Agustan 2020 ne Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya ke cikin shekara 79 a Duniya.

IBB @ 79: Wasu zababbun hotunan Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Ibrahim Badamasi Babangida kwanaki da danginsa
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta tsakuro maku wasu hotunan tsohon shugaban Najeriyar a lokacin da ya ke kan kujerar mulki da kuma a halin yanzu.

Ibrahim Badamasi Babangida ya yi mulkin Najeriya tsakanin 1985 zuwa 1993 a matsayin shugaban kasa na mulkin soja.

Janar Babangida ya shafe kusan shekaru 30 a gidan soja, ya na kuma da hannu a hambarar da gwamnati da-dama da aka rika yi.

IBB kamar yadda aka fi saninsa, mutumin jihar Neja ne, sai dai ana tunanin cewa iyayensa ainihi sun zo garin ne daga yankin Arewa.

Babangida ya na cikin wadanda su ka sadaukar da ransu wajen yakin basasa inda har aka yi yunkurin ganin karshen rayuwarsa.

KU KARANTA: Buhari ya taya IBB murnar cika shekara 79

IBB @ 79: Wasu zababbun hotunan Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Ibrahim Badamasi Babangida Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

IBB ya yi suna ne lokacin da aka kashe Murtala Mohammed inda shi kadai ya fuskanci shugaban ‘yan tawayen da su ka nemi juyin mullki.

Kafin ya zama shugaban kasa a watan Agustan 1985, Babangida ya rike mukamai a gidan soja har da shugaban sojojin kasan Najeriya a 1984.

A shekarar 2009 ne cutar daji ta kashe mai dakin tsohon shugaban watau Maryam Babangida wanda su ka shafe shekaru 40 tare.

Hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi ya fito da wani tsohon hoto da aka dauka a lokacin da Babangida ya ke bikin shekara 50.

An dauki wannan tsohon hoto ne a gidan gwamnati da ke Legas a wancan lokaci, kafin Babangida ya tattara ta dawo birnin tarayya Abuja.

Wannan hoton kwanan nan ne yayin da jikokin tsohon sojan su ka kai masa ziyarar sallah a garin Minna.

Shekaru 27 da barinsa mulki, Babangida ya tsufa har bai faye zirga-zirga ba, ya takaita rayuwarsa a katafaren gidansa da ke Minna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel