NSIP: Kwamitin majalisa ya yi karin haske kan rahoton binciken Osinbajo

NSIP: Kwamitin majalisa ya yi karin haske kan rahoton binciken Osinbajo

A ranar Talata ne kwamitin bincike a kan yadda aka kashe kudin jama'a ya bayyana cewa ba ya binciken ofishin mataimakin shugaban kasa ko kuma shi kansa Farfesa Yemi Osinbajo kamar yadda wasu rahotanni su ka wallafa.

Wasu kafafen yada labarai sun wallafa rahoton cewa kwamitin majalisa ya na binciken ofishin mataimakin shugaban kasa a kan zargin badakala da kudaden walwala da tallafawa 'yan kasa a karkashin shirin NSIP na gwamnatin tarayya.

Sai dai, shugaban kwamitin bincike na majalisa, Honarabul Wole Oke, ne ya sanar da hakan ranat Talata yayin da ya ke gabatar da jawabi a gaban babban sakataren ma'aikatar kudi, kasafi da tsare-tsare, Uwargida Olusola Idowu.

Oke ya bayyana cewa bincikensu ya karkata ne wajen samun hujjoji da bayanai a kan ciyar da dalibai 'yan makaranta da aka gudanar a karkashin shirin NSIP bisa jagorancin ma'aikatar kasafi da tsare-tsare.

"Bayanan da mu ka samu sun nuna cewa ofishin mataimakin shugaban kasa ne keda alhakin tsarawa da sa-ido a kan gudanar da aiyukan shirin NSIP.

"Amma batun bayar da kwangila aiki ne na ma'aikatar kasafi da tsare-tsare, wacce yanzu aka hade da ma'aikatar kudi.

"Shaidu sun nuna mana cewa ma'aikatar kasafi da tsare-tsare ne ke bayar da kwangilar aiyukan shirin NSIP tun daga shekarar 2016 har zuwa watan Satumba na shekarar 2019, lokacin da aka kirkiri ma'aikatar walwala da jin dadin 'yan kasa.

NSIP: Kwamitin majalisa ya yi karin haske kan rahoton binciken Osinbajo
Osinbajo
Asali: Twitter

"Abinda mu ke bukata a halin yanzu shine bayanan yadda ma'aikatar kasafi da tsare-tsare ta bayar da dukkan kwangiloli a karkashin shirin NSIP.

"Bincikenmu bashi da wata alaka da ofishin mataimakin shugaban kasa, ma'aikatar kasafi da tsare-tsare mu ke bincika," a cewar Oke.

DUBA WANNAN: N-Power: An bayyana mataki na gaba bayan 'yan Najeriya miliyan biyar sun nemi aikin

Ofishin mataimakin shugaban kasa ne ke kula da gudanar da shirin NSIP tun bayan fara shirin a shekarar 2016.

Amma daga baya, bayan zaben shekarar 2019, an mayar da shirin karkashin sabuwar ma'aikatar walwala, tallafi, da jin dadin 'yan kasa a karkashin minista Sadiya Umar Farouq.

Ofishin mataimakin shugaban kasa bai taba saka hannu a harkokin hada-hadar kudi ko bayar da kwangila a karkashin shirin NSIP ba.

Ma'aikatar kasafi da tsare-tsare ta kasa ce keda alhakin kasafi, tsarawa, bayar fda kwangila da fitar da kudaden da ake kashewa a karkashin shirin NSIP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel